Tsaro: Arangamar 'yan fashi da soji bayyi wa ja'iran dadi ba a yau

Tsaro: Arangamar 'yan fashi da soji bayyi wa ja'iran dadi ba a yau

- Tsageru sunyi arba da sojoji, inda wasu suka rasa rayukansu

- An kashe Tsageru, wasu kuma sun tsere cikin daji da raunuka sakamakon karon da sukayi da rundunar sojoji mai suna IDON RAINI a jihar zamfara

- Tsaro ya lalace a wasu jihohin kasar nan

Tsaro: Arangamar 'yan fashi da soji bayyi wa ja'iran dadi ba a yau
Tsaro: Arangamar 'yan fashi da soji bayyi wa ja'iran dadi ba a yau

Mataimakin daraktan jami'in hulda da jama'a na sojoji, Major Clement Abiade ya tabbatar da haka a Sokoto a ranar litinin, 14 ga watan Mayu 2018. Rundunar dai sunyi sintiri daga Dansadau zuwa sansanin tsagerun da ke kauyen gidan Kewoje dake karamar hukumar Maru da ke jihar zamfara.

"An ceto wata HALIMA, wacce sukayi garkuwa da ita. An duba sansanin kuma an tarwatsa shi." yace.

Yace abubuwan da aka samu sun hada da babur guda daya da kuma wayar tafi da gidan ka.

"Labari yazo mana cewa tsagerun na ta birne yan uwansu a kauyen NABANGO bayan da sukayi arba da rundunar."

Mai magana da yawun rundunar a Maradun yace wani wanda ake zargi mai suna Mohammed Usman wanda aka tabbatar yana kan hanyar shi ta zuwa Sokoto don karbo to wasu makamai don amfanin tsagerun jihar Zamfara daga wani Malam Yellow wanda aka cafke a gidan shi a Sokoto.

DUBA WANNAN: Anga watan Ramalana

Kayan da aka kwace sun hada da bindiga mai sarrafa kanta, wayoyin tafi da gidan ka guda biyar, da kudi Naira dubu dari da ashirin da biyar, da kuma faifan lumbar mota.

Major Abiade yace za a mika wadanda ake zargin da kuma kayayyakin da aka kama su dashi ga hukumar 'yan sanda domin bincike.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng