Hukumomin tsaro na shirin yiwa 'yan shi'a dirar mikiya muddin...
- 'Yan Shi'a na muzahara a Abuja da sauran birane
- Sun koka kan 'cin zali' wai da ake yi musu
- An yi musu kisan gilla, kuma hukumomi sun tsare shuwagabanninsu
Hedkwata Guards Brigade da ke garin Abuja, tace tana sane da zanga zangar lumanar da 'yan shi'a ke yi kullum a birnin tarayya kuma bazata yi kasa a guiwa ba gurin tura rundunar ta matukar abin ya wuce makadi da rawa.
Duk da dai a yanzu, abubuwan da kungiyar keyi basu kai ga a tura musu runduna ba amma tace suna nan suna kallon su kuma jira kawai sukeyi.
An tabbatarwa da mazaunan birnin tarayyan da kuma kewayenta cewa komai lafiya yake, sannan kuma su cigaba da gudanar da halastattun aiyukan su.
Kwamandan Guards Brigade, Birgediya Janar Umar Musa, ya bada tabbacin nan a wata tataunawa da yayi da manema labarai a wani bikin Brigade corporal wanda akayi a Mambila Barracks.
Janar Musa yace, sojoji da ke tsaron lafiyar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa da kuma kewayen Babban birnin tarayya suna sane da zanga zangar lumanar da 'yan shi'a ke yi kullum a Abuja. Suna bukatar a saki shugaban su wanda har yanzu yana gaban kuliya ne.
DUBA WANNAN: Tsaro ya inganta a Zamfara
Yace har yanzu harkokin kungiyar bai fi karfin 'yan sandar Najeriya, wadanda ke da alhakin kare lafiyar mutane da dukiyoyi.
Ya ja kunnen su da cewa, indai hangs zangar su tafi karfin yan sandan, to tabbas sojoji zasu shigo al' amarin da gaggawa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng