Yanzu-Yanzu: An ga wata a jahohi da dama na Najeriya - Sarkin musulmi
Labarin da ke iso mana daga majiyoyi da dama na nuni ne da cewa jama'a a jahohi da dama na Najeriya sun ga watan Ramada a farkon daren yau Laraba, 16 ga watan Mayu, shekarar 2018.
Wannan dai ta tabbata ne a cikin wata sanarwa daga bakin Sarkin musulmi inda ya tabbatar da ganin watan a jihohi da dama kuma hakan a bisa al'ada na nufin watan na Ramadana ya tsaya kenan.
KU KARANTA: An bankado badakalar Naira triliyan 8 a gwamnatin tarayya
Legit.ng dai ta samu cewa kasar Saudiyya ma ta bayar da sanarwar ganin jinjirin watan na Ramadana a kasar ta biyo bayan fakuwar da yayi ba'a gan sa ba a jiya.
Shi dai watan Ramadana yana da matukar falala a rayuwar musulmi inda suka yadda cewa Ubangiji Allah yana bude kofofin aljanna tare da rufe na wuta a lokacin.
Haka ma dai a watan Ramadana, musulmai kan kame bakin su daga cin abinci ko shan abin sha tare da kusantar iyali daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng