Karshen Motar kwadayi Tashar Wulakanci: An yankewa Leburan da ya saci Mazaunin Masai da hita wata 8 a kurkuku
- Garin neman gira ake rasa Ido inji masu iya magana, wani Lebura ya shiga tasku
- Kotu ta nuna ba sani ba sabo akansa bayan ya saci kayan aikin gida
Kotun Karmo dake garin Abuja ta yankewa wani Lebura mai suna Tarnisu Ibrahim da ya saci mazaunin ban daki da kuma na’urar dafa ruwan zafi hukuncin zaman gidan yari har na tsawon watanni takwas.

Ibrahim dai mazaunin gida mai lamba 62 ne a unguwar Galadima cikin Abuja, ya amsa laifuka biyun da ake tuhumarsa da su ba tare da batawa kotu lokaci ba, sannan ya nemi sassaunci.
‘Dan sanda mai gabatar da kara Dalhatu Zannah ya shaidawa kotun cewa wani mai suna Lazarus Yakubu ne ya kai kara zuwa ofishin ‘yan sandan dake Utako a ranar 9 ga watan Mayu.
KU KARANTA: Ramadan: Matar shekarau ta tallafawa mabukata da kuma zawarawa
Zannah ya ce, wanda ake zargin da abokan harkyallar ta shi su biyu sun hada baki ne wajen satar kayan, asirin shi Ibrahim din ya tonu ne yayin da abokan harkar tasa suka tsere suka bar shi. Kuma tun a yayi tuhuma ya amsa laifin nasa. A cewar jami'in.
A bisa haka ne alkalin kotun mai shari’a Abubakar Sadiq ya yanke masa hukuncin wata takwas a gidan yari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng