Ba arziki zan tafi nema a Majalisar Dattawa ba – Dr. Aliyu Tilde

Ba arziki zan tafi nema a Majalisar Dattawa ba – Dr. Aliyu Tilde

Wani Bawan Allah mai suna Aliyu Tilde wanda ya fito takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu ya bayyana muradun sa. Tilde na neman maye gurbin Marigayi Sanata Ali Wakili da ya rasu kwanaki.

Ba arziki zan tafi nema a Majalisar Dattawa ba – Dr. Aliyu Tilde
Aliyu Tilde yace ba zai karbi makudan alawus ba in ya zama Sanata

Dr. Aliyu Tilde ya sha alwashin cewa zai yi wa mutanen sa da su ka nemi yayi takara aiki idan har aka zabe sa a Majalisa. Tilde ya kuma bayyana cewa ba zai karbi wadannan mahaukatan alawus din da ake biya ba domin aikin kan sa.

Tilde a wani dogon jawabi da ya fitar a makon jiya yace zai rika amfani da albashin da yake bukata domin tafiyar da aikin ofis din sa ne kurum. Sanatan yace duk rarar da ya samu zai rika aikowa mazabar sa ne domin ayi kananan ayyuka.

KU KARANTA: Ayyukan da Buhari ya kaddamar a Jihar Jigawa

Babban Masanin kuma Marubuci zai dai tsaya takara ne a Jam’iyyar SDP ya kuma ce yana addu’ar ranar da ‘Yan Majalisar kasar za su daina karbar makudan kudi na facaka da sunan alashi. Aliyu Tilde yace ba kudi zai je nema a Majalisa ba.

A karshen makon can kun ji cewa Tsohon Gwamnan Bauchi Isa Yuguda ma zai fito takarar Sanatan Bauchi a karkashin GNP. Akwai wani tsohon ‘Dan Majalisar Jihar da shi ma ya fito takarar kujerar ‘Dan Majalisar Dattawan da za ayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel