Yaki da Cin Hanci da Rashawa abu ne mai matukar Wahala - Buhari

Yaki da Cin Hanci da Rashawa abu ne mai matukar Wahala - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da lamunin sa akan yadda yaki da cin hanci da rashawa ke da matukar wahala ta gasken-gaske.

A cewar shugaba Buhari, cin hanci da rashawa na da tasirin gaske rassa daban-daban na rayuwar mu wanda a yanzu wasu sun tsarkake cin amana daga cikin nau'ikan laifuka da suka dauke ta a matsayin harkar rayuwa ta yau da kullum.

A sanadiyar haka ne shugaba Buhari ke fafutikar sauya dabi'un da karfafa gwiwar 'yan Najeriya wajen dawowa kan turba ta gaskiya da rikon amana.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Daily Trust ta bayyana, shugaba Buhari ya yi wannan furuci a garin Abuja yayin kaddamar da sabuwar shelikwatar hukumar hana yaki da cin hanci da rashawa da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC.

Yaki da Cin Hanci da Rashawa abu ne mai matukar Wahala - Buhari
Yaki da Cin Hanci da Rashawa abu ne mai matukar Wahala - Buhari

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari tun hawan sa kujerar mulki a 2015 ya tabuka muhimmiyar rawar gani wajen yakar cin hanci da rashawa a mu'malai na al'ummar Najeriya musamman ma'aikatan gwamnati.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bayyana rawar da gwamnatin sa ta taka cikin shekaru 3

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, babbar manufa ta gwamnatin sa ita ce tabbatar da kare amanar al'umma wanda a yanzu yaki da cin hanci ya fara babakere ta ko ina a fadin kasar nan.

Jagoran na Najeriya ya kuma kirayi al'ummar kasa nan wajen goyon bayan hukumomi masu hana yiwa tattalin arziki zagon kasa domin nauyi yaki da cin hanci da rashawa ya rataya a wuyan kowa.

A yayin haka kuma shugaba Buhari ya nemi hadin gwiwar majalisar dokoki ta kasa wajen fafata wannan yaki na kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel