Labari mai dadi: Kasar Canada zata maida Najeriya ta daya a harkar hako ma'adanai

Labari mai dadi: Kasar Canada zata maida Najeriya ta daya a harkar hako ma'adanai

- Daya daga cikin manyan kamfanonin hakar ma'adanai na kasar Canada mai suna Thor Exploration, zai zuba babban hannun jari a Najeriya domin habaka harkar hakar zinari a farkon shekarar 2020

- Shugaban kamfanin yace, sun yanke hukuncin saka hannun jarin ne saboda yankin Afrika ta yamma suna kokarin bunkasa tattalin arzikinsu ta wasu hanyoyi wadanda ba na man fetur ba

Labari mai dadi: Kasar Canada zata maida Najeriya ta daya a harkar hako ma'adanai
Labari mai dadi: Kasar Canada zata maida Najeriya ta daya a harkar hako ma'adanai

Daya daga cikin manyan kamfanonin hakar ma'adanai na kasar Canada mai suna Thor Exploration, zai zuba babban hannun jari a Najeriya domin habaka harkar hakar zinari a farkon shekarar 2020, shugaban kamfanin yace, sun yanke hukuncin saka hannun jarin ne saboda yankin Afrika ta yamma suna kokarin bunkasa tattalin arzikinsu ta wasu hanyoyi wadanda ba na man fetur ba.

DUBA WANNAN: Wani dan Shi'a na gab da lashe zabe

Sakamakon faduwar kudin mai daga shekarar 2015-2016, bankin duniya yace zai bayar da kudi masu tarin yawa don taimaka Gwamnatin Najeriya gurin habaka hakar ma'adanai zinari wanda aka watsar dashi da dadewa.

Daya daga cikin shirye-shiryen kamfanin na Thor Explorations ya hada da kamfanin Segilola Gold Project da ke jihar Osun wanda shugaban kamfanin Segun Lawson yace, burinsu shi ne samar da zinari a wata uku na farkon shekarar 2020, kuma suna da wurin hakar zinari na kimanin ounces 500,000.

"A halin yanzu dai kamfanin na Thor Exploration yana kokarin habaka gurin hakar zinari na kasar," inji Lawson a wata hira da aka yi dashi a wayar tarho waya. Yace yana da lasisin hakar ma'adanai kuma zai samar da dala miliyan 72 farkon hakar.

Lawson ya siya kamfanin Segilola a shekarar 2016 a dala miliyan 3.1 kudi hannu, tare da hannun jarin Thor na dala miliyan 6.

Yayi alkawarin biyan kudin da gaggawa matukar aiki ya kankama.

Bankin duniya ya bayar da kusan dala miliyan 150 ga Gwamnatin Najeriya don habaka wasu bangarorin da ba na man fetur ba, bayan da tattalin arzikin kasar ya fadi sakamakon faduwar kudin man fetur, inda a yanzu haka kasar tana gab da farfadowa.

Tallafin bankin duniya dai, an bada shi ne don habaka bangaren hako ma'adanai wanda bana man fetur ba da kuma samar da abubuwan more rayuwa a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng