Matan Dapchi: Wanda aka tsare ta cika shekaru 15 da haihuwa a hannun Boko Haram

Matan Dapchi: Wanda aka tsare ta cika shekaru 15 da haihuwa a hannun Boko Haram

Leah Shu’aibu wanda ita kadai ce ragowar yarinyar da ‘Yan Boko Haram su ka sace a Makarantar Dapchi ta cika shekara 15 a Duniya a hannun ‘Yan ta’addan har yanzu babu labarin ceto ta.

Kwanakin baya dai aka sace ‘Yan makaranta fiye da 100 daga wata Makarantar Gwamnati a Garin Dapchi a cikin Jihar Yobe. Sai dai an yi dace an maido duka matan ban da wannan Baiwar Allah mai suna Leah Shu’aibu.

Matan Dapchi: Wanda aka tsare ta cika shekaru 15 da haihuwa a hannun Boko Haram
Leah Shuaibu tayi watanni wajen 'Yan Boko Haram

‘Yan Boko Haram din sun ki sakin Mis Leah Shu’aibu ne dalilin kurum ta ki karbar Musulunci kamar yadda ‘Yan uwan ta su ka bayyan. Shu’aibu dai Kirista ce kuma ta nuna cewa sam ba za tayi ridda daga addinin na ta ba.

KU KARANTA: Shugabannin baya su ka kawo cin hanci a Najeriya

Yanzu dai Mis Shu’aibu tana hannun ‘Yan ta’addan kuma ta cika shekara 15 da haihuwa a wajen su. Mun samu labari cewa a lokacin da Mahaifiyar ta ta ji labarin halin da ta ke ciki dai sai da ta suma saboda tashin hankali.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dai yayi alkawarin cewa Gwamnatin sa za ta ceto wannan yarinya kamar yadda aka ceto sauran ‘Yan matan. Sai dai har yanzu shiru ka ke ji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel