Falalar Ramadan: An ‘yanta fursinoni kusan dubu a Dubai
- Azumi na cigaba da gabatowa Jama'a na shirye-shiryen daura niyyar aiyukan alheri domin rabauta da falalar cikin watan
- Hakan ne ya sanya mahukuntan kasar Dubai su kayi afuwa ga mutanen kusan dubu daya domin su yi Azumi tare da iyalansu
A yau Litinin ne shugaban hadaddiyar daular Larabawa (UAE) Sheikh Khalifa Bin Zayed Al Nahyan, ya bayar da umarnin yin afuwa ga Fursunoni 935 domin su sake sabuwar rayuwa.
Wannan afuwa da akai musu ta biyo bayan gabatowar watan Ramadan na wannan shekara a wani yunkuri na basu damar fara rayuwa ko sun koyi darasi daga iftila’in da yayi sandiyyarsu zuwa gidan kurkukun. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar (WAM) ya rawaito.
KU KARANTA: Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram biyu yayin kubutar da wani tsoho
A duk shekara dai Musulmai na yin azumin sati hudu a duk shekara a watan Ramadan, watan da yake da mutukar tasiri da muhimmanci a rayuwar kowanne Musulmi.
Ana sa rai za’a fara Azumin wannan shekara ne nan da kwanaki biyu ko uku, wato za’a fara duban wata ne tun ranar Laraba.
Yin afuwa ga Fursunoni a Dubai dai tamkar wata al'ada ce a duk lokacin da Azumin ya kusanto domin neman tubarrakin fara Azumin cikin sa'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng