Abin takaici: Yunwa ta tuntsura mata suna tsince-tsincen hatsin da ya zube ƙasa
- An samu hoton mata na sharan hatsin da ya zube a Kasuwa
- Wannan abu ya tayar da hankalin mutane
Talauci da yunwa karuwa yake yi a fadin Najeriya musamman a Arewacin Najeriya kulli yaumin. Abin ya tashi daga rashin samun ingantaccen ilimi, hanyoyi masu kyau, wutan lantarki da ingatacciyar kiwon lafiya; yunwa yana hallaka jama'a.
Wannan yunwa bai bar wadanda ke karkara ko birane ba. Wani makaranci shafin Legit.ng Hausa ya nuna mana wasu hotunan wasu mata a Arewacin Najeriya wadanda aka gani suna sharan hatsin da ya zube a kasa suna bakace kasar domin yin abinci da shi.
Yace: "Mata A Kasuwa Saboda Yunwa Su Na Share Hatsin Da Ya Zube ƙasa Suna Sharewa Su Bakace Kasar Su Kai Anika Suyi Abinci Da Shi.
Ya Allah Ka Taimaka Ma Rayuwar Al'umma Karabata Da Wannan Bakin Talaucin Amin".
KU KARANTA:
A bangare guda, masu hannu da shuni na makwabtaka da irin wadannan mutane amma ba zasu taimaka musu ta hanyar fidda Zakkansu ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng