Kannywood: Abubuwan da baku sani ba game da Maryam Babban Yaro

Kannywood: Abubuwan da baku sani ba game da Maryam Babban Yaro

Maryam Gidado wacce aka fi sani da Maryam Babban Yaro ta kasance daya daga cikin mata da suka shahara a farfajiyar shirya fina-finan Hausa ta kannywood.

Maryam dai ta kasance bazawara domin ta taba yin aure har sau biyu. Tayi aurenta na farko a lokacin tana yar shekaru 13 a duniya kasancewar a al’adar Fulani ana aurar da yara mata da wuri.

Sannan kuma ta haifi yarta ta farko tana da shekaru 14 bayan shekara daya da aurenta kenan.

Haka zalika ta sake aure inda anan ne ta haifi danta na biyu. Sannan kuma ta bayyana cewa a lokacin da take da cikin dan nata na biyu ne sai mijin ya gudu ya bar ta.

Jarumar ta kuma bayyana cewa burinta ya cika a yanzu musamman a harkar fim sai dai kawai tana burin Allah ya bata miji nagari tayi aure.

KU KARANTA KUMA: 2019: Shugaba Buhari zai yi nasara Inji Minista Chris Ngige

Da aka tambayi jarumar batun yadda yan fim suka dauki lamarin aure tace:

“To, ai mu ba ruwan ido muke yi ba, muna tunanin maza suna ganin mu a fim ne, suna son su aure mu don wata manufa da suke da ita. Shi ya sa muke tsoron auren, ba wai muna tunanin wane mai kudi ba ne, ko marar kudi ba. Don idan ka auri mai kudi ma zai zaci don kudinsa ka aure shi. Gara ka auri talaka idan kudin ya zo kuna tare da shi. To yanzu abin ne sai ya zama muna tsoron mazan, su ma suna tsoron mu.”

Da aka tambayi jarumar ko tana wani kasuwanci baya ga harkar fim, Maryam tace:

“E, ina yin kasuwanci. Don yanzu ina da wajen gyaran gashi a gidanmu. Sannan a makarantarmu ina yin aiki na wucin gadi, kuma ina saro kayan mata ina sayarwa."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel