Son zuciya bacin zuciya: Yadda wasu matasa sun kashe kaninsu da duka akan rikicin wayar salula

Son zuciya bacin zuciya: Yadda wasu matasa sun kashe kaninsu da duka akan rikicin wayar salula

Wani matashi mai shekaru 17, Mahmud Adamu, ya gamu da ajalinsa a hannun yan uwansa uwa daya uba daya, sakamakon wata yar tirka tirka da ta taso game da wata wayar hannu, watau salula, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan uwanda Mahmud, wanda dalibi ne a makarantar sakandarin garin Minna, su biyu, Nura Adamu, yayansa uwa daya uba daya, da Hussaini Adamu, dan yayan mahaifinsa, suna casa shi ne bayan da suka nemi wata wayar salula suka rasa.

KU KARANTA: Yaki da yan bindiga: Yansandan Najeriya sun kama wani rikakken dan bindiga ‘Rambo’ a jihar Kaduna

Wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis din da ta gabata, a unguwar Kaje, dake karamar hukumar Chachanga na jihar Neja, inda sakamakon dan banzan dukan da Mahmud ya sha a hannun yan uwansa, ya zubar da jinni sosai.

Sai dai ganin yawan jinin da Mahmud ya fitar ne ya sa Hussaini da Nura suka ranta ana kare, inda suka bar shi kwance rai fakwai mutu fakwai, rai a hannun Allah.

Son zuciya bacin zuciya: Yadda wasu matasa sun kashe kaninsu da duka akan rikicin wayar salula
Wayar salula

Majiyar ta ruwaito daga bisan jama’a sun garzaya da shi Asibitin tunawa da Ar Alfa Alhaji Sule, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa, bayan sun kammala bicike akan gawar tasa kuma suka mika shi ga iyalansa don yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, ASP Muhammad Abubakar Dan Inna ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya bada tabbacin jami’an hukumar zasu kamo wadanda ake zargi da kisan ba da dadewa ba.

ASP Dan Inna ya kara da cew binciken gawar da likitoci suka yi ya nuna Mahmud ya rasu ne sakamakon matsaloli da ya samu a cikin jikinsa a dalilin dukan da ya sha a hannun yan uwansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: