Ni na koyawa Kwankwaso sa jar hula - Gwamna Ganduje

Ni na koyawa Kwankwaso sa jar hula - Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa da ma can shi ne ya kirkiro da manufar sanya jar hula shi da tsohon uban gidan sa Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso tare da mabiyan su tun lokacin suna jam'iyyar PDP.

A cewar gwamnan ya kawo shawarar ne domin su samu su bambance tsakanin masoyan su na zahiri da kuma masu yi masu adawa saboda rikicin da suke fama da su na cikin jam'iyya a wancan lokacin.

Legit.ng ta samu cewa har yanzu dai magoya bayan Sanata Kwankwaso din dake wakiltar shiyyar jihar ta Kano ta tsakiya na ci gaba da saka jar hular su inda a hannu guda kuma masu yi wa Gwamna Ganduje biyayya tuni suka watsar da tasu.

Ganduje, wanda ya zama gwamna a shekarar 2015 tare da goyon bayan Dakta Kwankwaso, ya ce ba kamar yadda 'yan Kwankwasiyya ke nuna wa ba, shi kwararren dan siyasa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel