Tsohon Gwamnan PDP zai fito takarar Sanatan Bauchi a karkashin GNP

Tsohon Gwamnan PDP zai fito takarar Sanatan Bauchi a karkashin GNP

Bisa dukkan alamu dai takarar kujerar Sanatan Kudancin Jihar Bauchi zai yi zafi don kuwa tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Isa Yuguda ya shigo cikin sahun masu neman kujerar a karkashin Jam’iyyar GPN mai adawa.

Mallam Isa Yuguda ya bayyana cewa zai yi takarar kujerar ‘Dan Majalisar Dattawan Jihar Bauchi a zaben da za ayi kwanan nan. Yuguda yace zai yi takara ne a Jam’iyyar GPN kamar yadda ya fadawa manema labarai a jiya.

Tsohon Gwamnan PDP zai fito takarar Sanatan Bauchi a karkashin GNP
Masu neman takarar kujerar Sanatan Bauchi sai sun dage

Isa Yuguda yace zai tsaya takarar ne bayan magoya bayan sa sun huro masa wuta ya nemi kujerar Sanata. Kwanakin baya dai tsohon Gwamnan ya bar Jam’iyyar PDP bayan yayi shekaru kusan shekara 8 yana Gwamnan Bauchi.

KU KARANTA: Wani tsohon ‘Dan Majalisa ya fito takarar kujerar Sanatan Bauchi

Shi ma dai Dr. Aliyu Tilde wani babban Marubuci kuma Masani a kan harkar Najeriya ya fito takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu. Kwanakin baya ne Sanata Aliyu Wakili wanda ke wakiltar yankin a Majalisa ya rasu kwatsam.

‘Yan takara sama da 30 ne ke harin kujerar Sanatan a karkashin Jam’iyyu kusan 4 da za su yi takara a zaben. Isa Yuguda zai yi takara ne domin taimakawa al’ummar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel