Al’umman Jihar Neja su na cabawa a Gwamnatin APC
Mun samu labarin irin alherin da Jihar Neja da ke Arewa ta tsakiyar Najeriya ta samu a Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Abdul-Baqi Ebbo wanda yana cikin Mukarraban Gwamnan Jihar Neja ya bayyana wannan.
Ayyukan da Gwamnatin Tarayya ta ke yi a Jihar Neja sun hada da aikin titi da na gada da dai sarau su. Daga cikin ayyukan dai da ake yi yanzu haka ko kuma ake shirin yi akwai:
KU KARANTA: Kayode Fayemi zai kara tsayawa takarar Gwamna a Ekiti
1. Ana fadada hanyar Suleja zuwa Garin Minna
2. Ana gina titin Garin Agaie zuwa Garin Baro
3. Ana gina gadar Tatabu
4. Ana gyara hanyar Kwantagoro zuwa Garin Makera
Bayan nan kuma an bada wasu sababbin kwangila 2 a Jihar:
5. Za a gyara hanyar Rijau tun daga Garin Kontogora
6. Za a gyara hanyar Garin Lambata zuwa Lapai
Haka zalika Gwamnatin Buhari na wani aikin na:
7. Yasan tashan ruwan Baro a Jihar ta Neja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng