Hukumomin Hisbah da FRSC sun tanadi Ma'aikata 830 domin ziyarar Buhari jihar Jigawa

Hukumomin Hisbah da FRSC sun tanadi Ma'aikata 830 domin ziyarar Buhari jihar Jigawa

Mun samu rahoton cewa hukumar Hisbah ta jihar Jigawa, ta tanadi ma'aikata 500 a sakamakon ziyarar aiki ta kwanaki biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar a ranar Litinin ta mako mai gabatowa kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Kwamandan hukumar Mallam Ibrahim Dahiru, shine ya bayar da wannan sanarwa yayin ganawar ranar Asabar din da ta gabata tare da manema labari a babban birnin jihar na Dutse.

Dahiru ya bayyana cewa, ma'aikatan za su hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro wajen bayar da ingataccen tsaro yayin ziyarar shugaban kasa.

Hukumomin Hisbah da FRSC sun tanadi Ma'aikata 830 domin ziyarar Buhari jihar Jigawa
Hukumomin Hisbah da FRSC sun tanadi Ma'aikata 830 domin ziyarar Buhari jihar Jigawa

Hakazalika jaridar The Punch ta ruwaito cewa, hukumar FRSC ta tanadi ma'aikata 330 gami da motocin kawo dauki na gaggawa 4 sakamakon ziyarar ta shugaban kasa kamar yadda shugaban hukumar na reshen jihar ya bayyana, Mista Angus Ibezim.

KARANTA KUMA: An kashe 'Yan ta'adda 18, 56 sun shiga hannu a jihar Kaduna

Hukumomin tsaron biyu sun yi tarayya wajen kira da gargadin al'ummar jihar akan kasancewa mutane na gari da kuma nuna hali na karamci da girmamawa yayin ziyarar shugaba Buhari.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, ana sa ran shugaba Buhari zai kaddamar da wasu sabbin manyan tituna biyar da kuma na cikin birni dake fadin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: