Sojin Saman Najeriya sun yaye sabbin dalibai masu tuqa sabbin jiragen da aka samo don yakar Boko Haram
- Hukumar sojin Najeriya ta saki hotunan sabbin zaratan sojinta na sama
- Zasu tuka sabbin jiragen da aka samo daga Amurka da Pakistan
- An maida kasashen yammacin Afirka wurin koyon taáddanci
Gafara Shekau ga maza nan bisa kanka', 'sojin Najeriya sun yaye sabbin daliban jiragen sama.
Hotunan dalibai da aka yaye a makarantar sojin sama ta NAF a jiya jumaá. Zasu tuka jiragen Super Mushshak Aircraft masu sabbin dabaru da naúrorin zamani wadanda ka iya ragargaza ramukan da Boko Haram ke buya.
Hukumarsojin kuma ta bude sabbin garejin adana da gyaran jiragen samanta wanda ake kira Hangar.
Daliban suna cikin dalibai 18 da aka dauka domin kwas din a jihar Kaduna, a barikin sojojin saman kasar dake Mando.
DUBA WANNAN: Zabukan LGs na Kaduna babu wani armashi
Har yanzu dai Najeriya na fama da mayakan Boko Haramun, da ma sauran burbushin masu tada zaune tsaye a sauran yankunan kasar nan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng