Zabukan kananan hukumomi na Kaduna basu yi wani Armashi ba
- Wasu na tsoron zabukan zasu zo da dabanci da tayar da zaune tsaye
- Akwai jamián tsaro kan kowacce akwatun zabe
- Unguwannin masu kudi babu kowa dake zabe, na talakawa kuma, tsiraru suka fito
Zaben da ake sa rai zai banbance wa ke da APC a jihar Kaduna yazo a yau asabar da tangarda a wasu wuraren na GRA dake Kaduna, inda jamaá babu wanda ya fito zaben sai jamián zabe da jamián tsaro harda na KASTELEA.
Zabukan dai sune zasu dora shuwagabannin kananan hukumomi a jihar, wanda baá yi ba tun bayan da jamíyyar APC ta amshe mulki a jihar a 2015.
Ya zuwa yanzu dai, saura baifi awa daya a tashi daga zaben ba, amma tsiraru ne kawai suka fita domin dangwala quriá a unguwannin da masu kudi suke.
DUBA WANNAN: Ya auri karamar yarinya amma ta kashe shi daren angonci
Unguwannin talakawa dai, an sami masu fita zaben, amma baá ga isowar jamián zaben da wuri ba.
An sanya dokar fita tun safe, shiru kake ji titunan birnin, ba kowa sai masu acaba da keke NAPEP a yau asabar.
Baá dai sani ba ko zaá iya magudin zabe a wannan karon, duk da yake zaben na inji ne, ba takardu ba, kamar yadda ake yi a baya a wasu jihohin.
Almajirai ne suka yi zabukan jihar Kano da aka yi a kwankin baya, bayan jamaá sunki fita kada quriun nasu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng