Ma’aikatan lafiyan Najeriya su na tserewa zuwa UK, US, UAE da Kanada

Ma’aikatan lafiyan Najeriya su na tserewa zuwa UK, US, UAE da Kanada

Bincike ya nuna cewa duk shekara dai Likitoci akalla 2000 ne ke barin Najeriya su tafi wata Kasar domin su yi aiki. Jaridar Guardian tace rashin albashi da kayan aiki ya jawo wannan matsala. Har Kasar Afrika ta Kudu Likitocin na zuwa aiki.

Ma’aikatan lafiyan Najeriya su na tserewa zuwa UK, US, UAE da Kanada
Likitoci na guduwa daga Najeriya zuwa kasar waje

Likitocin Najeriya kan bar Kasar su tafi irin su Kasar UAE da Amurka da Ingila da Kanada domin samun albashi mafi tsoka da kuma kwarewa a aiki. Idan aka cigaba da tafiya a haka nan da shekaru 5 dai Likitoci 10000 za su bar Najeriya.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban kasa IBB yayi wa Iyalin Isiaka Rabiu ta'aziyya

Bayan nan kuma aiki na yi wa Likitocin Najeriya yawa don kuwa harsashe ya nuna cewa Likita 1 yake kula da marasa lafiya 6000 a kasar. A irin su Amurka dai Likita 1 yana zaman marasa lafiya 500 ne, a Indiya kuma marasa lafiya 2000.

Likitcoin kasar nan sama da 5000 yanu haka su na Kasar Ingila su na aiki kamar yadda Hukumar NHS na Kasar ta Birtaniya ta bayyana a bana. Akwai dai kaso mai tsoka na Likitocin da ke Ingila da asalin su ‘Yan Kasar Najeriya ne.

Yanzu haka dai Ma’aikatan lafiya su na yajin aiki a Najeriya. Kuma idan ba ku manta ba kun ji cewa babban Jam’iyyar adawar Najeriya watau PDP ta fara hurowa Shugaban kasa Buhari wuta ya fito ya bayyana cutar da ke damun sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel