Gwamnatin Jihar Kano ta sauya Sunan Sabon Asibitin Yara da Sunan Marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u

Gwamnatin Jihar Kano ta sauya Sunan Sabon Asibitin Yara da Sunan Marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u

A yayin da a ranar Juma'ar da ta gabata ne aka gudanar da jana'iza inda aka sanya gawar Marigayi Khalifa Sheikh Isyaka Rabi'u a makwancinta, gwamnatin jihar Kano ta yiwa zakakurin malamin kyakkyawan karamci na din-din-din.

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sauya sunanan sabon asibitin yara dake daura da hanyar gidan Zoo a cikin birnin jihar da sunan Marigayin Malamin.

Wannan rahoto ya zo ne cikin wata sanarwa da sa hannun kwamishinan watsa labarai na jihar, Mallam Muhammad Garba da ya bayyana a ranar Juma'ar da ta gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin jihar Kano ta sauya sunan asibitin na Paediatric Hospital zuwa Khalifa Sheikh Isyaku Rabi'u Paediatric Hospital.

Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u wanda gawurtaccen dan Kasuwa ne kuma zakakurin Malamin Addinin Islama mai Inkiyar Khadimul Qur'an, ya rasu ne a ranar Talatar da ta gabata a wani asbitin birnin Landan bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya da zamto ajalin sa.

Marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u
Marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u

Kwamishinan ya bayyana cewa, majalisar zantarwa ta jihar ce ta bayar da lamunin wannan karamci da aka yiwa Marigayin Malamin yayin zaman ta da ta gudanar a ranar Alhamis din da ta gabata.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Sama ta kaddamar da wani Sabon Rukuni a Jihar Osun

Ya kara da cewa, Marigayi Khalifa ya samu wannan karamci ne sakamakon rawar da ya taka yayin rayuwar sa wajen bayar da gudunmuwa mara adadin wajen ci gaba karatun Al-Qur'ani da addinin Islama baya ga sadaukar da dukiyar sa ta hanyoyi daban-daban wajen kyatatawa al'ummar jihar.

A yayin da majalisar ke addu'ar jin kai ga Marigayi Isyaka Rabi'u, ta kuma kudirci ci gaba da yabo gami da jinjina wa macancanta a jihar da suke sadaukar da gudunmawar su wajen kawo ci gaba a cikin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: