Cikin Hotuna: Jerin Mutane 8 mafi karfin Iko a na Fadin Duniya a 2018
A yayin da akwai kimanin mutane biliyan 7.5 a ban kasa, wata sabuwar kididdiga da mujallar Forbes ta fitar a ranar Talatar da ta gabata ta bayyana yadda wasu mutane 75 ke da rinjayen tasiri wajen gudanar da al'amurra a duniya.
Wannan kididdiga da mujallar ta fitar ta bayyana yadda wadansu tsirarun mutane ke da karfin iko da suka dara na sauran al'umma sakamakon tarin dukiya, adadin mabiya, kujerar mulki da sauran ababe na arzikin duniya da suke da ita.
Rahotanni sun bayyana cewa, gawurtaccen dan kasuwa kuma hamshakin mai kudin nan na Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, shi kadai ne bakar fata kuma dan asalin kasar Najeriya da ya samu shiga cikin wannan jeranto da aka fitar a shekarar nan ta 2018, inda yake a mataki na 66 kamar yadda mujallar ta bayyana.
Cikin wannan jeranto da mujallar ta fitar Legit.ng ta kawo muku jerin hotunan mutane 8 daga cikin su mafi karfin iko da rinjayen tasiri a ban kasa kamar haka:
8. Muhammad Bin Salman Al Saud: Yariman Kasar Saudiyya
7. Bill Gates: Mai Kamfanin Microsoft da Melinda and Gates Foundation. Shine na Biyu a tarin Dukiya a duk fadin Duniya.
6. Pope Francis: Jagoran Mabiya Addinin Kirista na Katolika
5. Jeff Bezos: Mai Kamfanin Amazon kuma shine wanda yafi kowa kudi a duk fadin Duniya.
4. Angela Merkel: Shugaban Kasar Jamus
KARANTA KUMA: Taron Jam'iyya: Okorocha da shugabannin APC na Jihar Imo sun gana da Osinbajo
3. Donald Trump: Shugaban Kasar Amurka
2. Vladmir Putin: Shugaban Kasar Rasha
1. Xi Jinping: Shugaban Kasar Sin watau China
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng