Kashe-Kashen Benuwe: Wani Lauya yayi karar shugaba Buhari a gaban Kuliya, ya bukaci a zartar da Hukuncin Ta'addanci kan Makiyaya
Wani fitaccen lauya na birnin Makurdi a jihar Benuwe, Mathew Nyiutsa, ya shigar da korafi gaban kotun tarayya dake birnin Abuja da bukatar sa ta zartar da hukunci akan makiyaya a matsayin kungiyar ta'adda.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan lauya ya shigar da korafin sa inda ya game shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami a matsayin masu amsa wannan lamari na korafi a gaban kotun ta tarayya.
Cikin korafin sa mai lamba FHC/ABJ/CS/499/18, lauyan yayi gargadin cewa al'amurran da makiyaya ke gudanarwa a jihar Benuwe da kuma kungiyar Miyetti Allah na janyo barazana ta ta'addanci wanda ya sabawa dokar ta'addanci da aka gindaya a kasar nan tun a shekarar 2011.
Lauyan ya yi koken cewa, makiyaya na ci gaba da muzgunawa al'ummar jihar Benuwe ta hanyar kashe-kashe da wulakantar da dukiyoyin su wanda a yanzu sun gurbata rayuwar su da mamaye yankin su na zamantakewa da suka gada tun iyaye da kakanni.
Legit.ng ta fahimci cewa, lauyan yana neman kotu da ta yi nazari mai zurfi cikin al'amurran da suka wakana a jihar a tsakanin ranar 1 ga watan Janairun 2018 zuwa watan Mayu da rayuka sama da 200 suka salwanta.
KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Sama ta kaddamar da wani Sabon Rukuni a Jihar Osun
Rahotanni sun bayyana cewa, al'ummomin Guma, Logo, Makurdi, Gwer, Buruku, Tarka, Katsina-Ala da kuma Ukum na jihar Benuwe na cikin halin kakanikayi sakamakon harin makiyaya da suka afku.
A yayin haka kuma Lauya Mathew ya bukaci diyya ta kimanin N50m a sakamakon asara da hare-haren suka janyo a gare shi, inda a halin yanzu yake neman kotu ta kayyade rana ta fara sauraron karar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng