'Yan sanda 6 sun zage Kwanjin su kan wani Ma'aikacin Lafiya a jihar Kwara

'Yan sanda 6 sun zage Kwanjin su kan wani Ma'aikacin Lafiya a jihar Kwara

A daren ranar Larabar da ta gabata ne aka shiga cikin rudani yayin da wasu jami'an tsaro na 'yan sanda suka sauke gajiyar su kan wani ma'aikacin lafiya na asibitin Ughelli bisa tuhumar sa da rashin taimakon su cikin gaggawa wajen tarairayar wani mara lafiya da suka kawo.

Wannan lamari ya sanya fusatattun 'yan sandan suka yi barazanar harbin wannan bawan Allah, Blessing Oshiegbu, sakamakon rashin gaggawar kulawa da wani mara lafiya da suka kawo asibitin wanda daga aka gano abokin aikin su ne.

Wata ungozoma ta asibitin da ta yi shaidar wannan lamari ta bayyana wa manema labarai cewa, jami'an sun tarawa Blessing gajiya inda suka rufe da saukar mari da babu adadi sa'annan suka tilasta da tsinin bindigar si akan duban lafiyar abokin aikin su da suka kawo.

Rahotanni sun bayyana cewa, Blessing cikin lalama da sanyin rai ya nemi jami'an da suka agaza masa wajen shigar da marar lafiyan cikin asibiti da hujjar shi kadai zai gagare shi inda nan take suka farmasa da cewar aikin sa ne ba nasu ba.

'Yan sanda 6 sun zage Kwanjin su kan wani Ma'aikacin Lafiya a jihar Kwara
'Yan sanda 6 sun zage Kwanjin su kan wani Ma'aikacin Lafiya a jihar Kwara

Wani babban ma'aikaci na asibitin da ya tabbatar da afkuwar wannan lamari ya bayyana cewa, a halin yanzu dai Blessing ya samu matsala a kunnuwan sa ta yadda ba sa iya daukan sauti sakamakon duka da ya sha a fuskar sa.

KARANTA KUMA: Taron Jam'iyya: Okorocha da shugabannin APC na Jihar Imo sun gana da Osinbajo

Legit.ng ta fahimci cewa, yayin da wannan lamari ke afkuwa da yawan marasa lafiya sun nemi mafaka sakamakon barazanar 'yan sandan da bude wuta da bindigun su kamar yadda babban likita na asibitin ya bayyana, Dakta Moses Eyevweruvwu.

Rahotanni sun bayyana cewa, a yayin da tawagar shugabannin ma'aikatan lafiya na asibitin ta nemi ba'asi a ofishin 'yan sanda na Ughelli a ranar Juma'a ta yau, ba bu abin da ta taras face cin mutunci da kuma kora irin ta Kare daga shugaban 'yan sanda na reshen, Adepoju Ilori.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng