Da Ango yaje zaike ma 'yar mitsilar Amaryarsa, ta halaka shi, leka kuji me take gaya wa kotu

Da Ango yaje zaike ma 'yar mitsilar Amaryarsa, ta halaka shi, leka kuji me take gaya wa kotu

A ranar Alhamis dinnan ne wata babbar kotu a kasar Sudan ta yankewa wata yarinya 'yar shekara 19 hukuncin daurin rai da rai, sakamakon kashe mijinta da tayi domin yayi mata fyade.

Da Ango yaje zaike ma 'yar mitsilar Amaryarsa, ta halaka shi, leka kuji me take gaya wa kotu
Da Ango yaje zaike ma 'yar mitsilar Amaryarsa, ta halaka shi, leka kuji me take gaya wa kotu

A ranar Alhamis dinnan ne wata babbar kotu a kasar Sudan ta yankewa wata yarinya 'yar shekara 19 hukuncin daurin rai da rai, sakamakon kashe mijinta da tayi domin yayi mata fyade. Anyi kira ga shugaban kasar ta Sudan Omar Al-Bashir da yayi mata rangwame domin kuwa anyi mata auren dole ne kuma da yarinta a tattare da ita. Sannan kuma tayi hakan ne don ta kare mutuncin kanta.

DUBA WANNAN: Hisabin Kaduna da gwamnanta gobe ne, a zabukan LGs

Noura Hussain tace, mahaifinta shine ya tilasta mata auren Dan uwanta lokacin da take shekaru 16. Inda ta gudu, ta koma zama tare da wasu danginta na tsawon shekaru uku.

Ta koma gidan iyayenta da yake Khartoum ne a watan Afirilu bayan mahaifin nata yace an fasa auren,inda daga baya ta gane wayau aka mata domin kuwa ana ta shirin bikin ta bata sani ba.

Hussein tace ta hana mijinta kanta bayan auren, amma a kwana na shida yayi mata fyade bayan da 'yan uwanshi uku suka ririke ta.

Washegari, ya je kara mata fyade ne, tayi kokarin hanashi ta hanyar soka mishi wuka, inda ta kashe shi har lahira.

Wata kotun shari'ar musulunci ta kama Hussein da laifin kisan ganganci.

An ba lauyan ta damar daukaka kara a cikin kwanaki 15.

"A bisa ga Shari'ar musulunci, dangin mijin zasu iya karbar diyya ko kuma kotu ta hukunta ta ta hanyar kisa. Dangin shi kuwa sun zabi kisa akan diyya." inji Badr Eldin Salah, wani lauya mai kare hakkin bil adama na Nahiyar Afirka wanda yake kotun ranar da akayi shari'ar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel