Tsaro: 'Yansanda sun kama masu garkuwa da jama'a har talatin

Tsaro: 'Yansanda sun kama masu garkuwa da jama'a har talatin

- Tsaro ya tabarbare a kasar nan

- Talakka shi yafi ji a jika

- Wannan karoo a kudu aka kama miyagun

Tsaro: 'Yansanda sun kama masu garkuwa da jama'a har talatin
Tsaro: 'Yansanda sun kama masu garkuwa da jama'a har talatin

Hukumar 'yan sanda ta jihar Imo sun yi nasarar kama wasu gungun 'yan fashi da masu garkuwa da mutane kimanin su 30, hukumar ta kama su a iyakar jihar Rivers da jihar Imo.

Hukumar 'yan sandan kuma sun yi nasarar kwace wasu muggan makamai ciki kuwa harda bindigogi masu kirar AK47 guda biyar.

Hukumar ta samu nasarar kama 'yan ta'addar a dai-dai lokacin 'yan ta'addar suka fita yin ta'asar su, inda suka yi bata kashi da 'yan sandan, a karshe 'yan sandan suka samu nasara akan su.

Majiyar mu Legit.ng ta samu rahoton cewar da 'yan ta'addar suka fahimci cewar 'yan sandan sunci karfin su sai suka ranta ana kare suka shiga dajin Apan da Umuapu, inda suka gudu tare da wasu 'yan mata da suka yi garkuwa dasu ba dadewa da fitowar su. To sai dai kuma hukumar 'yan sandan sun samu nasarar kama da yawa daga cikin 'yan ta'addar.

Wata wacce 'yan sandan suka samu nasarar kubutar da ita daga wurin 'yan ta'addar wacce ta bayyana sunan ta da Ndidi Azonobi tace 'yan ta'addar sun tare motoci sama da 18 wanda suke dauke da matafiya kimanin 324, inda suka yi garkuwa da mutane 48 suka shiga dasu cikin daji suka kwace musu wayoyin su sannan suka yi wa wasu daga cikin su fyade.

Wani wanda aka yi abun gaban shi shima ya bada shaidar cewar wasu daga cikin 'yammatan da suka nuna taurin kai, 'yan ta'addar sun ji musu muggan rauni, inda a yanzu haka an garzaya dasu babban asibitin tarayya dake Owerri suna karbar magani.

Azonobi ta kara da cewar da yawa daga cikin mutanen da aka yi musu fashin dalibai ne na jami'ar jihar Imo dake Owerri, sannan kuma wasu daga cikin su 'yan kasuwa ne.

DUBA WANNAN: Bambanci tsakanin Gurguzu da Jari-Hujja

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Andrew Enwerem, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace yanzu haka hukumar tana yin iya bakin kokarin ta wurin gabatar da bincike.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng