Shehu Sani ya maida martani ga El-Rufai, yace gwamnan na bukatar ganin likitan mahaukata
Shehu Sani, Sanatan dake wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya bukaci gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yaje ya ga likitan mahaukata domin a duba kwakwalwarsa don a tabbatar bashi da tabin hanakali.
Sahara Reporters ta bayyana cewa Sani ya bukaci hakan ne a wata wasika day a aike ga babban daraktan likitoci, na asibitin mahauka dake jihar Kaduna wato, federal neuro-psychiatric hospital, Kaduna.
Legit.ng ta tattaro cewa wasikar wanda keda kwanan wata 7 ga watan Mayu ya bayyana cewa kalamun da El-Rufai keyi a yan kwanakin nan, inda ya bukaci mutanen jihar da su yaki sanatoci uku dake wakiltansu ya nuna cewa yana bukatar ganin likitan mahaukata.
Idan dai bazaku manta ba El-Rufai ya tsinewa sanatocin dake wakiltan jihar Kaduna bayan sun ki amince masa ya ciwo bashi a babban banin duniya.
A halin da ake ciki, a ranar Juma’a, 11 ga watan Mayu, Gwamana Nasir El-Rufai ya bayyana sanatocin dake wakiltan Kaduna a majalisar dokokin tarayya a matsayin tsinannu. El-Rufai ya bayyana cewa yan majalisan makiyan mutanen jihar Kaduna ne.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa har yanzu nike cigaba da sa jar hula - Gwamna Ganduje
A wani rubutu da gwamnan ya wallafa a shafin Facebook, ya ja ayoyin Qur’ani yayinda yake bayyana sanatocin a matsayin mayaudara kuma munafukai.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng