Yan bindiga sun hallaka mutane 3 yayin da suka kai wani mummunan hari a Masallaci
Ke duniya, ina zaki da mu ne, mun shiga wani irin zamani da mutane basu dauki ran mutum dan uwansu a bakin komai ba, sakamakon yadda ake wulakanta ran da Allah ya darajta, ta hanye kisan gilla kan dan matsalar da bata kai ta kawo ba.’
Jarida The cables ta ruwaito wasu gungun mahara dauke da muggan makamai da suka hada da bindigu da adduna sun far ma wani Masallaci a garin Durban dake kasar Afirka ta kudu, inda suka yi ma wasu Masallata guda uku yankan rago.
KU KARANTA: Ko ba mutuwa akwai tsufa: Wani tsoho mai shekaru 104 ya kai kansa ga halaka alhalin yana sane
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shaidun gani da sun tabbatar da cewar maharan da suka isa Masallacin wanda nay an Shi’a ne a cikin wata zuga sun danne wasu Masallata guda uku, inda suka yi amfani da wukakensu suka yayyanka makwagoronsu.
Wani jami’in Kaakaki yace: “Mahara su uku dauke da muggana bindigu sun yi amfani da wukake suka yi ma mutane yankan rago a Masallaci, sun bar wukarsu guda daya a wajen da suka kai harin.” Sai da ana tunanin babban Limamin Masallacin suke nema.
Haka zalika Kaakakin Yansandan Kwzulu Natal ya bayyana cewa: “Wani Masallaci dake garin Verulam, yanki Kwazulu Natal nisan kimanin mil 15 daga birnin Druban ya gamu da hari, inda suka banka ma wasu dakuna wuta, bayan sun yanka mutane uku,a yanzu mutum daya ya mutu, yayin da suaran biyu ke cikin halin ha’ulai’.”
Daga karshe Kaakakin yace har yanzu ba’a tabbatar da manufar kai harin ba, kuma basu kama ko mutum da yaba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng