An sake kwatawa: Wani ma’aikacin gwamnati ya aikata ma kansa sabalikita saboda rashin samun albashi a Kogi

An sake kwatawa: Wani ma’aikacin gwamnati ya aikata ma kansa sabalikita saboda rashin samun albashi a Kogi

Matsalar rashin biyan albashi da ma’aikata ke fama da shi a wasu johohin Najeriya ya rikirkita musu lissafi, musammam saboda gaza biyan bukatunsu da na iyalansa, hadi dsa zafin yanayi da ake ciki, gami da tsadar rayuwa.

Wadannan matsaloli da ake jerosu, wadanda ma’aikatan da basa samun albashinsu ka iya fuskanta su kan jefa da dama daga cikinsu mawuyacin hali, wand aka iya kai ga sun tafka wasu munanan ayyuka da nufin biyan bukata, ko kuma su nemi kawo karshen rayuwarsu da kansu.

KU KARANTA: Ko ba mutuwa akwai tsufa: Wani tsoho mai shekaru 104 ya kai kansa ga halaka alhalin yana sane

A nan ma jaridar Rariya ce ta kawo labarin wani ma’aikacin gwamnati a jihar Kogi dake fuskantar matsalar rashin samun albashinsa na wata da watanni, inda ya kwashe tsawon lokaci yana jiransa hakkinsa, amma shiru kake ji kamar mushuriki ya ci shirwa ya sha ruwa.

An sake kwatawa: Wani ma’aikacin gwamnati ya aikata ma kansa sabalikita saboda rashin samun albashi a Kogi
Ma'ikacin

Sai dai karancin hakuri na wannan ma’aikaci ya kai ga ya yanke shawarar daukan ransa da kansa, inda ya rataye kansa a wani daji dake jihar Kogi, sai dai dayake yana sauran kwana a gaba, sai Allah ya kawo wasu jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa, FRSC, inda suka yi kicibus da shi yana reto a sama.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito abinka da jami’an ceton rayuka, nan da nan suka bazama, suka yi ta maza, suka kwanto wannan bawan Allah da yayi yunkurin halaka kansa, dama bahaushe yace zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai ya yi.

Wannan dai ba shi ne farau ba game da batun kashe kai da wasu ma’aikatan gwamnati ke yi a jihar Kogi, inda a ko a shekarar data gabata sai da wani mai mukamin Darakta ya hallaka kansa sanadiyyar rashin biyansa albashin gomman watanni.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel