Wani Mai Laifi ya yiwa Alkaliyar Kotu Barazanar ta yi kankanta ta tura shi Gidan Wakafi

Wani Mai Laifi ya yiwa Alkaliyar Kotu Barazanar ta yi kankanta ta tura shi Gidan Wakafi

Wani lamari mai kamanceceniya da wasan kwaikwayo ya afku a wata Kotun Kasar Zimbabwe, yayin da wani mutum da ake tuhuma da laifi ya yi barazana ga alkaliyar Kotun, Caroline Tafira, inda yake ganin ba ta da damar zartar masa da hukunci kasancewar jinsin mace.

Tatenda Mkanganwi, wani mazaunin kauyen Tabuzgaidzwa da ake zargi da laifin fyade ya fusata a gaban kotu da har sai da jami'an tsaro suka dakatar da shi da yi masa shinge.

Wani Mai Laifi ya yiwa Alkaliyar Kotu Barazanar ta yi kankanta ta tura shi Gidan Wakafi
Wani Mai Laifi ya yiwa Alkaliyar Kotu Barazanar ta yi kankanta ta tura shi Gidan Wakafi
Asali: UGC

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, wannan mutumin ƙauye ya shaidawa alƙaliyar kotun cewa ta yi masa ƙanƙanta wajen zartar da hukuncin a kansa gami da cewa don dai kurum ba ta da masaniya a kansa ne take neman gwada masa hali irin na yaran yau.

KARANTA KUMA: Amurka ta ba Najeriya N32bn don gudanar da ƙididdigar masu cutar Kanjamau

Legit.ng ta fahimci cewa, cikin tsawa da tayar da jijiyar wuya Tatenda ya shaidawa alkaliyar kotun majistiren cewa, ta yi matuƙar ƙanƙanta ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan waƙafi domin ci ga da sauraron ƙarar sa zuwa wani lokaci na gaba.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta iHarare ta kasar Zimbabwe ta ruwaito, Alkaliya Tafera ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Tatenda inda kuma ta bayar da umarnin Likitoci su dubi lafiyar sa kafin a sake dawo da shi gaban kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel