Tsakanin dan adam da kudi: Ya kashe mahaifiyar sa, ya kwakule mata zuciya da ido daya domin yin tsafin kudi

Tsakanin dan adam da kudi: Ya kashe mahaifiyar sa, ya kwakule mata zuciya da ido daya domin yin tsafin kudi

'Yan sanda a jihar Anambra sun damke wani mutum, Christopher Okadigbo; mai shekaru 52 saboda yin amfani d sassan jikin mahaifiyar sa domin yin tsafi.

Jaridar Nigeria News ta rawaito cewar Christopher ya hada baki da wani abokin sa, Mista Ameke Udolu, domin kashe mahaifiyar sa, Roseline Okadigbo; mai shekaru 80 a duniya tare da cire mata zuciya kwakule mata idon ta na hagu domin yin tsafi.

Babban dan marigayiyar, Innocent Okadigbo, ya bayyana cewar dama mahaifiyar ta su ta taba sanar da shi a kan rashin amincewar ta da ziyarar da abokin kanin sa ke kawowa gidan, musamman irin abubuwan da suke tattaunawa yayin hira, amma bai taba daukan hakan a matsayin barazana ga rayuwar ta ba saida ya samu kiran abin da ya faru tukunna.

Tsakanin dan adam da kudi: Ya kashe mahaifiyar sa, ya kwakule mata zuciya da ido daya domin yin tsafin kudi
Cibiyar tsatsuba

"Ranar 1 ga watan Mayu mahaifiyar mu ta kira ni t shaida min cewar tana tsoron kwana a gidan ta saboda abinda ta ji Christopher da abokin sa na tattaunawa, in ji Innocent.

DUBA WANNAN: An kori wani jibgegen alkali daga aiki, an fara binciken wasu 7

Sannan ya cigaba da cewa, "a ranar 2 ga watan Mayu sai na samu kira daga wani mai suna Pius Aniefule mutumin da ya shaida min cewar an samu gawar mahaifiya ta male-male cikin jini. Bayan ya kira ni ne saina samu kira daga dan uwa na Christopher, duk da cewar ya yanke hulda da ni tun shekarar 1999, tare da shaida min cewar mahifiyar mu ta mutu, sannan ya ce shi ma kiran sa aka sanar da shi saboda baya gari, ya yi tafiyar zuwa jihar Neja."

Asirin Christopher ya tonu ne bayan anyi nasarar kama abokin sa, Udolu, yayin da yake kokarin guduwa daga gidan marigayiyar, inda suka yanka ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel