Sai dai kuyi hakuri amma bakuda hurumin gayyatar IGP - Falana ga Majalisa
- Femi Falana babban lauya mai zaman kansa, yace majalisa batada hurumin kiran Ibrahim Idris shugaban hukumar ‘Yan Sanda
- Majalisar ta bayyana cewa shugaban hukumar ‘Yan Sandan bai cancanci rike wani matsayi ban a gwamnati sakamakon kin amsa kiran da sukayi masa har sau uku
- Majalisar ta kira shugaban hukumar ‘Yan Sandan ne sakamakon matsolin tsaro da ake fuskanta a kasar sannan kuma da lamarin Sanata Dino Melaye, wanda a yanzu haka yake hannun hukumar ta ‘Yan Sanda
Femi Falana babban lauya mai zaman kansa, yace “majalisa bakuda hurumin ku kira Ibrahim Idris shugaban hukumar ‘Yan Sanda a matsayin makiyin mulkin farar hula”.
Majalisar ta bayyana cewa shugaban hukumar ‘Yan Sandan bai cancanci rike wani matsayi na gwamnati ba sakamakon kin amsa kiran da sukayi masa har sau uku.
Majalisar ta kira shugaban hukumar ‘Yan Sandan ne sakamakon matsolin tsaro da ake fuskanta a kasar sannan kuma da lamarin Sanata Dino Melaye, mai wakiltar Kogi ta yamma, wanda a yanzu haka yake hannun hukumar ta ‘Yan Sanda.
Idris ya tura wakili a madadinsa a lokuta biyu da majalisar ta kirashi, amma majalisar taki amincewa da sauraren wakilin wanda ya tura.
Lokacin da yake jawabi a Channels TV Falana, yace majalisar tayi kuskure data kawo lamarin Sanata Melaye a cikin sha’anin kiran da sukayiwa shugaban hukumar ‘Yan Sandan.
KU KARANTA KUMA: Majalisa bata da hurumin kiran shugaban kasa ko Gwamnoni domin tsayawa su bayyana a gabanta - Falana
Yace duk da kisan da akeyi a kasar shugaban hukumar ‘Yan Sandan ba shine wanda ya kamata ace majalisar ta kira ba domin ya mata bayani game da hakan, ministan cikin gida da kuma Atoni-Janar sune wadanda ya dace majalisar ta kira.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng