An kama Almajirai 92 a jihar Kano

An kama Almajirai 92 a jihar Kano

- A jiya ne hukumar Hisbah ta jihar Kano tace ta kama Almajirai masu bara akan tituna sama 92 a cikin birnin Kano, saboda zargin su da sabawa dokar da jihar ta gindaya akan hana barace-barace akan tituna a birnin jihar

An kama Almajirai 92 a jihar Kano
An kama Almajirai 92 a jihar Kano

A jiya ne hukumar Hisbah ta jihar Kano tace ta kama Almajirai masu bara akan tituna sama 92 a cikin birnin Kano, saboda zargin su da sabawa dokar da jihar ta gindaya akan hana barace-barace akan tituna a birnin jihar. Jami'in hukumar Hisbah din mai kula da bangaren masu kama mabaratan, Dahiru Nuhu, yace hukumar ta kama mabaratan da misalin karfe 1 na dare, a kasuwar 'Yankura da kuma tashar 'Yankaba.

DUBA WANNAN: Magoya bayan Atiku zasu hada gagarumin taro a Abuja

A cewar sa, 89 daga cikin wadanda aka kama din, Almajirai ne, wadanda keda shekaru 12 zuwa 19, ya kara da cewar mafi yawancin mabaratan sun fito ne daga yankin jihohin Bauchi, Borno, Kaduna, Kebbi, Katsina da kuma Jamhuriyyar Nijar.

Gwamnatin jihar Kano, karkashin Hukumar Hisbah, ta saka dokar hana barace-barace akan tituna, inda tayi gargadin cewar zata kama duk wanda ta kama da laifin karya dokar da gwamnatin ta saka.

Duk mabaratan da hukumar ta kama, tun daga lokacin da hukumar ta saka dokar, duk wanda ba dan jihar Kano bane hukumar tana tusa keyar su zuwa jihohin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel