Na shiga ban dauka ba: Wata mai aikin gida ta saci gwalagwalai na Miliyoyin Nairori

Na shiga ban dauka ba: Wata mai aikin gida ta saci gwalagwalai na Miliyoyin Nairori

- Dubun wata 'yar aiki ya cika, ta shiga komar 'Yan sanda

- Idon wata yar aiki ya raina fata bayan da aka gurfanar da ita gaban kiliya bisa zargin sace kayan Miliyoyi

A Ranar 9 ga watan Mayun wannan shekara ta 2018 da muke ciki ne aka gurfanar da wata mai suna Happiness Denis a gaban wata kotu dake Ikeja a Jihar Legas, bisa zargin yiwa uwar gidanta sama da fadi da wasu sarkoki gwalagwalai wadanda darajar kudinsu ya kai kimanin Naira Miliyan Arba'in da bakwai 47M.

Denis mai shekaru 28 da haihuwa wadda ke zaune da uwar gidanta rukunin gidaje na Isauro dake yanki Lekki a jihar Legas, an tuhume sa da aikata laifuka har guda biyu wato hadin baki da kuma satar kayan uwar gidansa.

Na shiga ban dauka ba: wata mai aikin gida ta saci sarkokin gwalagwalai na Miliyoyin Nairori
Na shiga ban dauka ba: wata mai aikin gida ta saci sarkokin gwalagwalai na Miliyoyin Nairori

Dan sanda mai gabatar da kara Benson Emuerhi, ya bayyanawa alkali cewa wadda ake zangirn ta hada baki da wasu ne domin aikata wannan laifi tun a ranar 12 ga watan Maris da ya gabata ne. Ya cigaba da bayyanawa kotun cewa Denis ta shiga dakin baccin uwar gidan nata ne, inda ta sace sarkokin mallakin Mrs. Ubena Obiageli.

KU KARANTA: Daya daga cikin 'yan fashin offa ya shigo hannu, ashe tsohon dan sanda ne

"Wanda ake zangirn da aikata laifin ta dade tana aiki a gidan amma bayan aikata halin Bera da ta yi sai ta gudu daga gidan. Kadan daga cikin kayan da ta sata sun hada da Agogon hannu, Sarkar wuya da kuma Awarwaro da kuma sauran wasu kaya masu matukar amfani.

'Yan sanda sun yi nasara kamo ta ne bayan da uwar gidan nata ta kai kara gun 'yan sanda inda ta bayyana musu abinda ya auku".

Wannan laifi ya saba ka'idar kudin laifuka na Jihar Legas karkashin sashi na 287 da kuma sashi na 411 na kudin manyan laifuka na 2015, wadda ake zangirn mutukar laifin ya tabbata zata shafe tsawon shekaru uku a gidan yari.

Na shiga ban dauka ba: wata mai aikin gida ta saci sarkokin gwalagwalai na Miliyoyin Nairori
Na shiga ban dauka ba: wata mai aikin gida ta saci sarkokin gwalagwalai na Miliyoyin Nairori

Sai dai wadda ake zangirn taki amincewa da laifin da ake tuhumarta da shi.

Alkalin kotun, Mrs. O. Sule Amzat, ta bada belin wadda ake tuhumar akan kudin Naira 500,000 da kuma mutum biyu wadanda zasu tsaya mata.

Alkalin ta bayyana cewa wanda zasu tsayawa wanda ake zargin dole su kasance 'yan uwanta sannan dole ne su zama suna da shaidar biyan harajin shekaru biyu da suka wuce ga gwamnatin jihar Legas.

Kana kuma ta dage zaman kotun har sai zuwa 30 ga watan Yulin wannan shekara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel