Za'ayi gwajin kwakwalwa ga matasan da ke son shiga aikin dan sanda

Za'ayi gwajin kwakwalwa ga matasan da ke son shiga aikin dan sanda

A jiya ne hukumar yan sandan Najeriya tace za'a gudanar da gwajin kwakwalwa ga duk matasan da ke son shiga aikin dan sanda a Najeriya, an dauki wannan mataki ne saboda a guje daukan wadanda za su rika harbin mutane babu gaira ba dalili.

Kazalika, za'a gudanar da gwaji don binciko wadanda ke shaye-shayen miyagun kwayoyi wanda suma hukumar ta ce ba za ta dauki duk wanda aka samu yana ta'amuli da miyagun kwayoyin ba.

Za'ayi gwajin kwakwalwa ga matasan da ke son shiga aikin dan sanda
Za'ayi gwajin kwakwalwa ga matasan da ke son shiga aikin dan sanda

Mataimakin Sufetan yan sanda na sashin bayar ha horaswa, Emmanuel Iyang ne ya bayar da wannan sanarwan a jiya yayin da ya ziyarci inda ake tantance masu sha'awar shiga aikin na dan sanda a kwallejin yan sanda da ke Ikeja a Legas.

KU KARANTA: Dalibai sun ragargaji malaman su saboda sun hana su satar amsa yayin jarrabawar WAEC

Kamar yadda Iyang ya bayyana, an kasa tantancewar zuwa gida uku ne, da farko za'a duba wadanda ke da credit a kalla a darusa guda biyar a jarabawar kamalla sakandire wanda suka hada da lisafi da turanci, sannan ba za'a dauki duk wani mai wata irin irin nakasa ba ko matsalar rashin gani.

A kashi na biyu na tantancewar daliban za su rubuta wata jarabawa da hukumar JMAB zata gudanar inda kowa zai sami sakamakon jarabawar nasa a nan take. Wanda sukayi nasarar cin jarabawar kuma zasu sake fuskantar wasu gwaje-gwaje don tabbatar da lafiyarsu.

Shugaban kwallejin, Kwamishinan yan sanda, CP Akinpelu Gbemisola ya ce ba za suyi kasa a gwiwa ba wajen bin dukkan tsare-tsaren da hukumar ta kafa wajen daukin sabbin yan sandan kamar yadda babban sufetan yan sanda, Ibrahim Idris ya bayar da umurni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164