Jana’izar Sheikh Isiyaka Rabiu: Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ranar hutu
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ranar Juma’a 24 ga watan Sha’aban, da ya yi daidai da 11 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu don baiwa al’ummar jihar damar halartar jana’iza tare da jimamin rashin Shehin Malami Isiyaka Rabiu.
Legit.ng ta ruwaito Malamin, kuma hamshakin dan kasuwa ya rasu ne a Talata, 8 ga watan Mayu a wani Asibiti dake birnin Landan, inda ya yi jinya, yana mai shekaru 93 a rayuwa.
KU KARANTA: Mutuwar Isiyaka Rabiu: Mu mahaddata mun yi rashi, Attajirai ma sun yi rashi – Dahiru Bauchi
Kwamishinan watsa labaru na jihar Kano, Muhammed Garba ne ya sanar da hutun a ranar Laraba 9 ga watan Mayu, inda yace: “An sanya ranar juma’a ne a matsayin ranar hutu don a baiwa jama’an jihar halartar jana’izar mamacin.”
Gwamnatin jihar ta sanar da gawar mamacin zata iso Najeriya a ranar Alhamis 10 ga watan Mayu, sa’annan a gudanar da jana’izar tasa a filin masallacin juma’a dake gidansa a Goron Dutse, da misalin karfe 2:30, bayan an yi sallar Juma’a.
Sheikh Isiyaka Rabiu, Khalifan Tijjaniya a nahiyar Afirka ya mutu ya bar matansa da yara 42, daruruwan jikoki da tattaba kunne da dama, da fatan Allah ya jikansa da gafara. Amin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng