Wani Malamin Islama ya fadi irin karamar babban Limamin Iran Khamenei
- Karamar Shaihunnai dai mabiyansu kawai ke iya gani
- Wani Malami yace Limamin Iran wanda yai shugaban kasa karfi ya hango 'gobe'
- Wai ya gano dama Amurka zata yaga wannan yarjejeniya ta Nukiliya da aka cimma a baya
Wani babban malamin addinin Islama a kasar Iran, Sheikh Kazem Sadiqi, ya ce shugaban tafiyarsu ta Shia tuni a baya ya hango dama cewa wannan abokantaka da kasashen waje kan shirin nukiliyar Iran, zai ruguje.
Kasashen Yamma ne suka shiga yarjejeniyar a 2015, bayan shekaru ana tattaunawa, inda aka sami matsaya, aka kuma sakar ma Iran din mara kan batun takunkumai da aka qaqaba mata.
Shehun Malamin, ya bayyana yadda cikin irin hangen nesa da karamar babban Limamin Sheikh Khamenei, ya hanga cewa wannan yarjejeniya zata ruguje wata rana.
DUBA WANNAN: Ta'aziyyar shugaba Buhari ga Kanawa
Shugaba Trump ne ya kekketa yarjejeniyar ya dawo da dukkan takunkumai da kasarsa ta sanya wa kasar ta Farisa.
Kasashen Turai dai sunce su baza su janye ba, haka ma kuma kasashen Larabawa masu makwabtaka da Iran din da Israila sun nuna farin ciki da wannan ci gaba.,
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng