Ko kunsan me janyewar Amurka daga yarjejeniyar Iran ke nufi ga Gabas ta Tsakiya?

Ko kunsan me janyewar Amurka daga yarjejeniyar Iran ke nufi ga Gabas ta Tsakiya?

- Kasar Israila ta dawo halayyarta ta juya shugabannin Amurka

- Turawa sun guji wani sabon katsalandan sun bar Amurka ita kadai

- Iran zata sake ballewa ta zama 'mai qaya baki hadiyuwa'

Ko kunsan me janyewar Amurka daga yarjejeniyar Iran ke nufi ga Gabas ta Tsakiya?
Ko kunsan me janyewar Amurka daga yarjejeniyar Iran ke nufi ga Gabas ta Tsakiya?

A kokarinta na hada Amurka rigima da wata kasar ta musulmi, kasar Israila, ta tabbatar ta goyi bayan duk wani wanda jam'iyyar Republican masu son addinin Kiristanci irinsu Bush, fiye da wanda jam'iyyar su Obama da Clinton ta tsayar, watau masu son a yi sulhu.

A yanzu dai, shugaba Trump ya dawo da tsohuwar basasa ta ruwan sanyi da AMurka keyi da kasar Iran, wadda aka shafe shekaru kusan 40 ana tafkawa da Farisawa masu Shi'a.

Rigimar, ta kunshi yadda tsohon shugaba Obama da kasashen Turai suka shawo kan Iran da ta hakura da son kera makamai na nukiliya, domin a sami fahimtar juna a yankin gabas ta tsakiya.

Sai dai hakan ya kau, bayan da a yanzu shugaba Trump ya janye daga yarjejeniyar da aka shafe shekaru ana sulhuntawa tsakanin sashen, sulhu da Israila taki jini.

DUBA WANNAN: Turkiyya ta mayar da martani kan kiran ayi gyara kan Qur'ani

Ita dai kasar ta Israila, bata son kasar ta Iran ta mallaki duk wani babban makami da ka iya lahanta ta, musamman ganin kasar ta Iran ta yarda da wani hadisi mai kiran da Musulmi su bi wani, wai Mahdi da zai zo haka kawai ya karkashe Yahudawan duniya.

Wannan kokari da Iran take yi, kokari ne na ta shirya ajje makamai wai don Idan shi Mahdin ya bulla ya taras musulmi sun shirya don a kar Kafirai, lamari da Turawa ke gani Iran ke son cimma ta hanyar yaudara.

A hannu daya kuma, kasashen Larabawa, basu son kasar Iran din wadda ta tsani irin nasu addinin da siyasar ta Sunni, wanda ka iya janyo musu yaki na gaba-da-gaba, musamman idan kananan kasashen yankin suka farga suka daina bari ayi amfani da kasashensu wajen wannan yakin.

A yanzu dai, wannan mataki na Amurka zai bakantawa limaman Iran wadanda su kuma zasu so su rama ta hanyar ingiza wasu yake-yaken ko na ta;adda ko na sunquru, ko ma cin dunduniyar Amurkar da Israila.

Tabbas kuma kasar Iran zata iya dawo da shirin na nukiliyar a boye, musamman idan kasashen Turai suka dawo suka mara wa Amurka baya, wanda hakan kan faru bisa al'ada.

Ko Israila bata kai hari Iran ba, tana iya zuga wani sususun shugaba a wata kasar mai karfi domin ya tumbuke mata mulkin Ustazai na Iran.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel