Dangote ya sake shiga jerin fitattun mutane 75 a duniya
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya sake shiga daga cikin jerin fitattun mutane 75 daga cikin yawan al'ummar duniya na kusan Biliyan bakwai da rabi.
Wannan ba shine karo na farko da attajirin dan kasuwar ke shiga wannan rukun ba, domin akan haka ne ya samu inkiyar da akeyi masa na mai kudin Afrika.
A cikin jerin Fitattun mutane 75 da mujallar Forbes ta fitar na wannan shekarar, Dangote ne kadai sunansa ya fita daga Nahiyar Afrika.
Sannan kuma shine ya zama mutum na 66 wanda ya shige gaban Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence.
KU KARANTA KUMA: 2019: Matasa 10,000 sun tsayar da Lamido a matayin dan takarar shugabancin kasa a PDP
A kullun dai arzikin Dangote na kara habbaka inda ake ganin hakan nada nasaba da tarin taimako da yakeyiwa mutane musamman yan gudun hijira da harin Boko Haram ya ritsa dasu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng