Farashin Man Fetur ya tumfaya a Kasuwannin Duniya, Amurka ta janye alakar ta da Kasar Iran
Farashin man fetur a kasuwanni duniya ya tumfaya da kaso biyu bisa dari a ranar Laraba ta yau yayin da shugaban kasar Amurka ya yi watsi da wata yarjejeniyar makamin nukiliya da ya kulla da kasar Iran kuma ya sha alwashin daukar mataki akan ta.
A ranar talatar da ta gabata ne shugaban kasar Amurka ya toshe kunnuwan sa daga sauraron roko na jin kai yayin da ya yi watsi da yarjejeniya da kasar Iran da aka kulla ta tun a shekarar 2015 da gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari na tattare da barazanar rikici a yankin daular Larabawa ta gabas da kuma rashin tabbaci gami da kokwanto kan wadatuwar man fetur sakamakon tsanani da ya yi a kasuwannin duniya.
Kwararrun kididdiga sun bayyana cewa, a sakamakon yiwuwar gazawar kasar Iran na fitar da man fetur zuwa kasashen duniya ya sanya farashin sa ya tumfaya a halin yanzu, inda manyan kasashe irin su China suka dogara a kanta wajen saye.
KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Masu Garkuwa da Mutane sun shiga hannun hukumar 'Yan sanda a jihar Benuwe
Legit.ng ta fahimci cewa, kasar Iran ita ce kasa da take sama wajen fitar da man fetur zuwa kasashen ketare a shekarar 2016 da ta gabata, sai dai a halin yanzu ta kasance kasa ta uku da take take bayan kasar Saudiyya da kuma Iraq.
A halin yanzu dai akwai yiwuwar wannan hukunci da kasar Amurka ta zartar na janye hannun ta daga yarjejeniyar zai tabbatar za ta dauki kwakkwaran mataki cikin kwanaki 108 muddin ba a sake kulla wata yarjejeniyar ba kamar yadda kadar watsa labarai ta NAN ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng