Yanzu Yanzu: Ma’aikatan lafiya na jiha zasu shiga yajin aiki tare da na tarayya

Yanzu Yanzu: Ma’aikatan lafiya na jiha zasu shiga yajin aiki tare da na tarayya

- Kungiyar ma’aikatan lafiya ta JOHESU tace ta umurci jami’anta na jiha da kananan hukumomi dasu shiga yajin aikin suma tare da jami’an lafiya na tarayya a yau Laraba

- Biobelemoye Joy Josiah, ciyaman na JOHESU, yace sun yanke shawarar hakan ne bayan ganawar da sukayi da gwamnati don magance matsalolin da suke fuskanta, amma ba wani muhimmin sakamako

- JOHESU kungiya ce ta jami’an lafiya banda Likitoci, wanda suka shiga yajin aiki sati uku kenan yau, sakamakon han ma dakunan awo da gwajegwaje ma duk an rufesu saboda ba ma’aikatan da zasu kula dasu

Kungiyar ma’aikatan lafiya ta JOHESU tace ta umurci jami’anta na jiha da kananan hukumomi dasu shiga yajin aikin suma tare da jami’an lafiya na tarayya a yau Laraba.

Biobelemoye Joy Josiah, ciyaman na JOHESU, yace sun yanke shawarar hakan ne bayan ganawar da sukayi da gwamnati don magance matsalolin da suke fuskanta, amma ba wani muhimmin sakamako daga gwamnantin.

JOHESU kungiya ce ta jami’an lafiya banda Likitoci, wanda suka shiga yajin aiki sati uku kenan yau, sakamakon han ma dakunan awo da gwajegwaje ma duk an rufesu saboda ba ma’aikatan da zasu kula dasu, sannan kuma babu masu daukar bayanin marasa lafiya.

Yanzu Yanzu: Ma’aikatan lafiya na jiha zasu shiga yajin aiki tare da na tarayya
Yanzu Yanzu: Ma’aikatan lafiya na jiha zasu shiga yajin aiki tare da na tarayya

Marasa lafiya sunfi shiga damuwa sakamakon kananan ma’aikatan asibi masu kula dasu da unguwar zoma da suka shiga yajin aikin wadanda sune muhimmai a kungiyar ta JOHESU, kuma duk suna cikin wadanda aka shiga yajin aikin tare dasu a asibitocin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Ciyaman na jam’iyyar PDP ya mayarwa da El-Rufa’i da martani bisa ga tsinuwa da yayiwa Sanatocin jihar Kaduna

Kungiyar ta bukaci sauran jami’anta na jiha da kananan hukumomi dasu shiga yajin aikin suma domin ya zamanto matsi ga gwamnatin tarayya don ta biya masu bukatarsu ta ‘Karin albashi’.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel