2019: Matasa 10,000 sun tsayar da Lamido a matayin dan takarar shugabancin kasa a PDP
Kungiyar matasa masu goyon bayan Lamido, wato Sule Lamido Youth Mobilization of Nigeria (SLYMN) sun bayyana cewa kimanin matasa 10,000 cikin miliyan daya na mambobinsu su sanya hannu don tsayar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido a matsayin dan takarar shugaban kasa a PDP na zabe mai zuwa a 2019.
Kungiyar sun bayyana hakan ne ta hannun shugabanta na kasa, Abdulhadi Abdullahi Sani (Cokali) lokacin kaddamar da ita tare da gabatar da mujalla a Jerrotel Hotel dake Jos a ranar Laraba.
Alhaji Sani ya bayyana cewa kungyar wacce aka kusan sama da shekara daya da watanni biyar da suka shige na da mambobi sama da miliyan daya a fadin jihohin Najeriya.
Ya kara da cewa kungiyar na bukatar sa hannu samma da miliyan guda domin ta kai babban sakatariyar PDP na kasa sannan kuma tayi kokarin ta sanya tawagar jam’iyyar su zabi Lamido a matsayin dan takararsu a zaben 2019.
KU KARANTA KUMA: Ana musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da gwamna Ajimobi
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ciyaman na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, Hassan Hyat, ya mayarwa da El-Rufa’I martini bisaga tsinewa Sanatocin jiha Kaduna da yayi.
Hyat yace duk wanda ya tsinewa sanatocin shima kansa tsinuwar zata hau kansa, ya fada hakan ne a Zankwa dake karamar hukumar Zangon Kata, lokacin da suke bikin cin abinci na wadanda suka dawo jam’iyyar daga APC.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng