Kannywood: Na yi da nasanin auren Sani mai iska – Fati Muhammed

Kannywood: Na yi da nasanin auren Sani mai iska – Fati Muhammed

Tsohuwar fitacciyar jarumar nan ta kamfanin shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Fati Muhammad, ta bayyana auren jarumi Sani Musa Mai Iska a matsayin babbar nadamar ta a rayuwa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da jaridar Blue Print inda ta bayyana cewa ta amince da cewa kowa na da jarabawar da Allah ya ke yi masa sannan kuma tace ita ta bangaren aure Allah ya jarabe ta.

Jarumar ta kara nanata maganarta da tayi a baya inda tace ba fa zata kara auren dan fim ba koma wanene kuwa.

Kannywood: Na yi da nasanin auren Sani mai iska – Fati Muhammed
Kannywood: Na yi da nasanin auren Sani mai iska – Fati Muhammed

Daga karshe kuma jarumar ta bayyana jarumi Ali Nuhu a matsayin wanda take darajawa fiye da kowa a masana’antar fim.

KU KARANTA KUMA: Hanyoyi 5 da mace zata mallaki miji cikin sauki

Idan za ku iya tunawa, Fati Muhammad, ita ce ta fito a cikin tsohon fim din nan na Sangaya tare da jarumi Ali Nuhu, a matsayin Zubaina, wannan fim din nan ya fito da ita.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel