Ciyaman na jam’iyyar PDP ya mayarwa da El-Rufa’i da martani bisa ga tsinuwa da yayiwa Sanatocin jihar Kaduna
- Ciyaman na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, Hassan Hyat, ya mayarwa da El-Rufa’I martini bisaga tsinewa Sanatocin jiha Kaduna da yayi
- Hyat yace duk wanda ya tsinewa sanatocin shima kansa tsinuwar zata hau kansa, ya fada hakan ne a Zangon Kataf
- El-Rufa’i a ranar juma’ar data gabata ya tsinewa Sanatocin jihar Kaduna bisaga kin amincewa da karbar bashin bankin duniya na $350m
Ciyaman na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, Hassan Hyat, ya mayarwa da El-Rufa’I martini bisaga tsinewa Sanatocin jiha Kaduna da yayi
Hyat yace duk wanda ya tsinewa sanatocin shima kansa tsinuwar zata hau kansa, ya fada hakan ne a Zankwa dake karamar hukumar Zangon Kata, lokacin da suke bikin cin abinci na wadanda suka dawo jam’iyyar daga APC.
El-Rufa’i a ranar juma’ar data gabata lokacin bayyana Buhari a matsayin dan takarar jam’iyyar APC na shugaban kasa, ya tsinewa Sanatocin jihar Kaduna bisaga kin amincewa da karbar bashin bankin duniya na $350m, inda ya bayyana su a matsayin makiyan al’umma.
Sanata Shehu Sani na APC mai wakiltar Kaduna ta tsakiya da Suleiman Hunkuyi na APC mai wakiltar Kaduna ta arewa sai kuma Danjuma Laah na PDP mai wakiltar Kaduna ta kudu, sunki amincewa da karbar bashin akan cewa jihar Kaduna itace ta biyu a cikin jihohin kasar nan data fi kowa bashi.
KU KARANTA KUMA: Masu kula da shugaba Buhari na boye rashin lafiyarsa – PDP
Hyat yace mutane sunji dadin yanda sanatocin suka ki amincewa da karbar bashin. Bayan haka ya bukaci kowa ya zama cikin shiri da katinsa na zabe zuwa ranar Asabar da za’a gudanar da zaben kananan hukumomi na jihar.
A halin da ake ciki, Jam’iyyar PDP ta zargi masu kula da shugaba Muhammadu Buhari kan cewamsun zabi su boye lamarin rashin lafiyarsa wadda takici taki cinyewa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng