Turnuku: An kwashi yan kallo a wani hari da Sojoji suka kai ma Yansanda a Legas

Turnuku: An kwashi yan kallo a wani hari da Sojoji suka kai ma Yansanda a Legas

Wasu jami’an Yansandan Najeriya dake Ofishin Yansanda na Badia, unguwar Ijora na jihar Legas sun dambace da wasu Dakarun Sojin ruwan Najeriya, a ranar Talata 8 ga watan Mayu, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito fadar doki in doke-kan tsakanin jami’an hukumomin da yayi sanadiyyar samun rauni na wasu Yansanda biyu, Sajan Tunde da Mogbojuri, ya janyo mummunan cunkoson ababen hawa a kan titin Apapa-Wharf road.

KU KARANTA: Mai martaba Sarkin Katsina ya nada sabon Babban Limamin jihar Katsina

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa Sajan Tunde yafi samun rauni a jikinsa a sakamakon dan banzan duka da Sojojin suka lakada masa, inda suka yayyaga masa kayan aiki.

Turnuku: An kwashi yan kallo a wani hari da Sojoji suka kai ma Yansanda a Legas
Rikicin Sojoji da Yansanda

Rahotanni sun bayyana cewar rikicin ya samo asali ne kan su waye zasu dinga lura da tafiyan ababen hawa akan titin ta hanyar bayar da hannu? Musamman ganin yadda Yansandan suka gaza kawar da cunkoso akan hanyar, hakan ne ya sanya Sojojin daukar gabaran gudanar da aikin.

Shaidan gani da ido yace Sojojin ruwa dake aiki a BEECROFT sun so titin ne a cikin wata motar akori kura, mai lamba GGE 499 DZ, dake dauke da sunan OP MESA rubuce a jikin motar, ganin hakan ya sanya Yansandan tserewa daga bakin aikinsu, inda Sajan Tunde ya je ya kai rahoton lamari zuwa ofishinsu.

Nan da nan shugabar Ofishin Yansandan tare da rakiyar Sajan Tunde,DSP Talabi da Sufeta Ausquo suka rankaya zuwa Ofishin Sojojin dake Area B bayan samun rahoton dalilin kaurewar fadar, don jin dalilin Sojojin na dukan jami’anta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng