Kasafin kudin 2018: An hurowa Majalisar Tarayya wuta bayan wata 6

Kasafin kudin 2018: An hurowa Majalisar Tarayya wuta bayan wata 6

Mun samu labari cewa Jama’an Najeriya sun fara kokawa da ‘Yan Majalisar Tarayya a kan kasafin kudin wannan shekarar. Yanzu dai an dauki fiye da rabin shekara amma Majalisar kasar ba ta amince da kasafin kudin banan ba.

Kasafin kudin 2018: An hurowa Majalisar Tarayya wuta bayan wata 6
Majalisa tayi shiru da batun lasafin kudin 2018

A makon nan ne aka gana a fadar Shugaban kasa tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da Shugabannin Majalisar kasar. Tun a Ranar 6 ga Watan Nuwamban bara aka mika kundin kasafin kudin shekarar 2018 amma har yanzu ba a sa hannu ba.

Daya daga cikin masu ba Gwamnan Jihar Neja shawara watau Mu’awiyya Muye yace ya kamata Majalisa tayi wa mutanen kasa bayanin inda kasafin wannan shekara ya shige. Muye yake cewa Majalisa tana kokarin kawowa Buhari matsala.

KU KARANTA: Gwamnatin Shugaba Buhari ta tona asirin Jonathan

Wani Bawan Allah mai suna Ayourb ta shafin sa na Tuwita yake cewa Jama’ar kasar sun yi shiru har yayi yawa don haka ya kamata yanzu a fara tambayar ‘Yan Majalisar Najeriya a ji ina aka kwana game da batun kasafin wannan shekarar da ake ciki.

Jama’a da dama irin su Grand Pa @Lawalyd sun nemi ‘Yan Majalisun Kasar su su yi wa mutanen da su ka zabe su bayani game da kundin kasafin kudin na bana. Mista Echeune wani mai kishin kasa shi ma dai ya nemi jin inda kundin kasafin ya shige.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel