Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa

- Nahiyar Afrika, yanki ne da ya yi kaurin suna wajen zaben tsofaffin mutane domin yin shugabanci duk da ana yiwa matasa kirarin "Shugannin gobe", amma hakan ba shi da wani tasiri musamman idan aka yi duba da mutanen da suke shugabanci a wasu kasashen dake Nahiyar ta Afrika.

- Ga kadan daga cikin shugabannin da kuma adadin shekarun haihuwarsa:

1. Beji Caid Essebsi – Tunisia (shekaru 92)

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa
Shugaban Kasar Tunisia Beji Caid Essebsi

An haife shi 29 ga watan Nuwamba 1926, Beji shi ne mutum na farko da aka fara zaba a matsayin shubagan kasar ta Tunusia, ya dare karagar mulki ne tun yana da shekaru 87. A baya kuma ya yi Ministan harkokin kasashen wajen tun daga 1981-1987, sannan ya yi Firaminista daga watan Fabrairu 2011 zuwa Disambar 2011. Bayan saukar shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe, ya kasance shi ne shugaba na biyu a yankin Afrika mai tarin shekaru.

2. Paul Biya – Cameroon (shekaru 85)

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa
Shugaban Kasar Cameroon Paul Biya

Paul haifaffen kasar Cameroon ne, kuma an haife shi 13 ga watan Fabrairu 1933. Ya kasance mutum ne wanda yake kaunar abinda ya shafi siyasa kuma ya yi gwagwarmaya da dama wanda daga bisa ya dare mulkin kasar tun 6 ga watan Nuwambar shekarar 1982. Yanzu haka yana cigaba da shugabanci da shekaru 85 wanda ya sa ya zamo mutum na 2 a yankin Afrika mai tarin shekaru, sannan na 10 a duniya baki daya.

3. Abdelaziz Bouteflika – Algeria (shekaru 81)

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa
Shugaban Kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika

An haife shi 2 March 1937 a kasar Algeria, kuma shi ne mutum na biyar da ya shugabanci kasar. Abdelaziz ya yi Ministan harkokin kasashen waje daga 1963-1979 , sannan shi ne wanda ya kawo karshen yakin basasa da aka yi a kasar a shekara 2002, ya rike mukamai da dama wanda suka hada shugaban kungiyar gamayyar kasashen duniya.

4. Manuel Pinto da Costa – São Tomé and Príncipe (shekaru 81)

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa
Shugaban Kasar São Tomé and Príncipe - Manuel Pinto da Costa

An haife shi a 5 Agusta 1937, Pinto ya kasance mutum na farko da ya fara darewa kan karagar shugabanci kasar Sao Tome and principe daga 1975-1991, ya sake lashe zabe a shekara ta 2011. Ya kasance mutum na hudu a jerin shugabannin da suke da yawan shekaru.

5. Alpha Condé – Guinea (shekaru 80)

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa
Shugaban ƙasar Guinea – Alpha Condé

An haife shi a 4 ga watan Maris shekara ta 1938, Alpha Conde shahararren dan siyasa ne a kasar Guinea wanda aka zabe shi a shekara ta 2010. Conde ya yi kokarin hambarar da shugaban kasar Lassana Conte har sau biyu daga karagar mulki a shekara ta 1993 da kuma 1998, sai dai yunkurinsa bai cimma nasara ba. Amma daga bisani ya zamo mutum na farko da aka zaba a matsayin shubagan demokaradiyya.

6. Peter Mutharika – Malawi (shekaru 77)

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa
Shugaban ƙasar Malawi–Peter Mutharika

Peter Mutharika ya kasance Shubagan kasar Malawi ne bayan rasuwar shugaban kasar a shekara ta 2012, ya zama shugaban ne a shekara ta 2014, kafin zamansa shugaban kasar ya rike mukamai da dama wanda suka hada da mai baiwa tsohon shugaban kasar shawara, har wa yau ya rike mukamai a hukumomi daban-daban na cikin gida da kuma kasashen waje kamar su; hukumar Adalci ta duniya, da kuma kungiyar lauyoyi ta duniya.

KU KARANTA: Barin zance: 'Yan sanda sun cafke wani Malamin Coci a dalilin yada kalaman kiyayya

Shi ma dai ya kasance mutum mai tarin shekaru wanda har yanzu yana shugabanci.

7. Muhammadu Buhari – Nigeria (shekaru 75)

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa
Shugaban ƙasar Najeriya-Muhammadu Buhari

Buhari ya dare mulki ne a shekara ta 2015 bayan rashin samun nasara da ya yi a zabukan da aka gudanar a shekarar 2003, 2007, 2011. Muhammadu Buhari a baya ya shugabanci kasar a karkashin mulkin soja inda ya yi nasara ta hanyar juyin mulki, inda ya yi shugabancinsa daga 1983-1985.

8. Nana Akufo-Addo – Ghana (shekaru 73)

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa
Shugaban ƙasar Ghana – Nana Akufo-Addo

An haifi shugaban a 29 Maris 1944, ya samu nasarar zama shugaban kasar bayan kayar da John Mahama da ya yi a zaben 2017 da aka gudanar. Kafin zamansa shugaban kasar ya rike mukamai da suka hada da Atoni Janar na kasar daga 2001-2003, sannan ya yi Ministan harkokin kasashen waje daga 2003-2007. Sannan ya yi rashin nasara a zabukan shugabancin kasara da aka gudanar a shekara 2008 da kuma 2012.

9. Yoweri Museveni - Uganda

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa
Shugaban ƙasar Uganda - Yoweri Museveni

Yoweri Museveni yana daya daga cikin mutanen da suka kasance yan adawa ga gwamnatin Idi Amin (1971-1979) da kuma Milton Obote (1980-1985), wanda ya yi sanadin hambarar da gwamnatin da ta gabata. Museveni yana da shekaru 73 na haihuwa wanda a yanzu ya yi sauye-sauye ga tsarin shugabancin kasar wanda suka ba shi damar cigaba da shugabantar kasar a halin yanzu.

10. Alassane Ouattara – Ivory Coast (shekaru 73)

Shugabanni ƙasashe 10 da suka fi tsufa a Nahiyar Africa
Shugaban ƙasar Ivory Coast- Alassane Ouattara

An haife shi a 1 Janairun shekara ta 1942 a kasar Ivory Coast dake yankin Afrika. Alassane ya zama shugaban kasar a shekara ta 2011, kafin nan ya rike mukamin Firaministan kasar daga shekara ta 1990-1993. Alasanne ya zama dan takara bisa inuwar jam'iyyar siyasa ta Republican (RDR) a shekara ta 1999, daga bisani ya lashe zaben da aka gudanar, sannan aka rantsar da shi a matsayin shubagan kasar a 4 ga watan Disambar shekarar 2010.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng