Da duminsa: Rundunar sojin sama sun ragargaji yan Boko Haram a Koleram
Rundunar sojin saman Najeriya sun ragargaji yan ta’addan Boko Haram a wani hari da suka kai musu jiya Litinin, 7 ga watan Mayu, 2018 a dajin Koleram.
Kakakin hukumar, Adesanya Adetokunbo, ya bayyana hakan ne a cikin wata jawabin da ya saki da safen nan. Yace:
“Wani jirgin hukumar sojin saman Najeriya Alpha Jet a jiya 7 ga watan Mayu 2018 ya hallaka yan Boko Haram yayinda suke taimakawa sojin kasa.
An kai wannan hari mai nasara ne bisa ga umurnin kwamandan 8 division cewa dakarun sojin da ke shara a Koleram sunyi arangama da yan Boko Haram.
Jami’an rundunar sojin saman suka shiga aiki inda fara tattaunawa da jami’an sojin kasa da ke artabu da yan Boko Haram. Kawai jirgin sojin yayi ruwan aradu kan mabuyar Boko Haram din inda ya hallakasu tare da makamnsu.”
Rundunar sojin saman Najeriya da na kasa sun kasance suna hada karfi da karfe wajen tabbatar da cewa an kawo karshen wannan ta’addanci da yan Boko Haram keyi a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
KU KARANTA: Buhari zai yi ganawar gaggawa da Saraki, Dogara a yau
A bangare guda, hukumar sojin saman Najeriya ta gudanar da bikin murnar cika hukmar shekaru 54. Daga cikin shirye-shiryen da ya gudana domin murnan shine pareti, wasa da jirage da kuma kaddamar da sabbin jiragen da aka sayo daga kasar Rasha.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng