Inda ranka: Yamutsi bayan da gwaggwon biri ya biyo wani manomi har gida a jihar Kuros Ribas

Inda ranka: Yamutsi bayan da gwaggwon biri ya biyo wani manomi har gida a jihar Kuros Ribas

Al'ummar garin Bitiah Irruan dake a karamar hukumar Boki ta jihar Kuros Ribas sun shiga rudani biyo bayan wani gwaggwan biri da ya biyo wani manomin kauyen har gida bayan ya dawo daga gona a ranar Juma'ar da ta gabata.

Kamar dai yadda muka samu, wani ma'abocin anfani da kafar sadarwar zamani ta Facebook mai suna Osang Gabriel ne ya shelanta hakan a shafin sa inda kuma ya bayyana cewa hakan ya ja hankalin al'ummar kauyen sosai da ma makwafta.

Inda ranka: Yamutsi bayan da gwaggwon biri ya biyo wani manomi har gida a jihar Kuros Ribas
Inda ranka: Yamutsi bayan da gwaggwon biri ya biyo wani manomi har gida a jihar Kuros Ribas

KU KARANTA: Kiristocin Najeriya sun sa kafar wando daya da Buhari

Legit.ng ta samu cewa yanzu haka dai komai ya fara lafawa a kauyen amma labarin na cigaba da yaduwa tare kuma da daukar hankali a sassa daban daban a fadin kasar nan.

A wani labarin kuma, Wata sambaleliyar budurwa mai suna Dami ta fallasa yadda ta ce wani mijin aure a Najeriya ya bukaci ta sadaukar masa da kanta ya kwanta da ita kafin ya bata aiki a kamfanin sa a kafar sada zumuntar zamani ta Tuwita.

Sambaleliyar budurwar dai ta bayar da wannan labarin ne tana kuma mai shawartar sauran 'yan uwanta mata da su maida hankali wajen neman na kansu musamman ma sana'a domin kaucewa fadawa irin tarkon maza da ta ce ta fada.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng