Wani Direban Tirela ya debo ruwan dafa kansa

Wani Direban Tirela ya debo ruwan dafa kansa

- Garin neman shan lagwada Direban Tirela na shirin shiga uku

- Bayan da yayi awan gaba da kayan mutane, yana gaban alkali yana shan tuhuma

Sakamakon satar duro goma na Kalanzir da aka kiyasta kuɗin kan Naira N560,000 da wani Direban Tirela yayi mai suna Ibrahim Wasiu ya shiga tasku.

A ranar Litinin ne dai aka kai Mutumin mai shekaru 32 gaban alkalin kotun dake Ikeja domin amsa tuhuma.

Wani Direban Tirela ya debo ruwan dafa kansa
Wani Direban Tirela ya debo ruwan dafa kansa
Asali: UGC

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ASP Ezekiel ya shaidawa kotun cewa, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 28 ga watan Maris a yankin Ogaba dake jihar Lagos.

Ya ce, Direban ana tuhumarsa ne da yin sama da faɗi da duro har 10 na Kalanzir da kimar kuɗinsa ta kai N560,000 mallakar Mr. Quadri Taiwo.

Kuma ana zargin dai ya sayar da kalanzir ɗin ne ga wasu Mutane biyu kana ya tsere.

Yanzu haka dai ana tuhumar Direban ne da loda kalanzir a motar da kawai kayan lemo ake dora mata, wanda hakan ya saɓa da dokar aikin kamfanin nasu tare kuma lalata mota wanda kuɗin gyara kawai sai da taci Naira N800,000.

KU KARANTA: Kisan da akeyi don a kunyatar da gwamnatinka ne – Sarkin Katsina ga Buhari

Wannan dalili ne yasa mai kayan Taiwo tare da masu Motar suka kai ɓarawon ƙara ofishin Ƴan sanda kara, su kuma suka 'Yan sandan suka damke shi.

Wannan laifi dai ya saba da sashi na 287(7) da 350 na kundin manyan laifuka na jihar Lagos.

Mutuƙar dai kotu ta tabbatar da ya aikata wanann laifi da ake zarginsa da shi, hukincin shekaru bakwai ne kamar yadda sashi na 287(7) sannan kuma da ƙarin wasu shekaru biyu na lalata musu motar da yayi kamar yadda sashi na 350 ya bayyana.

Amma sai dai Direban ya ƙeƙasa ƙasa ƙeme-ƙeme wajen yarda da aikata laifin, a dalilin haka ne alƙalin kotin mai shari'a Uwargida B.O. Osunsanmi ta bayar da belinsa kan kuɗi Naira N200, 000 tare da waɗanda zasu tsaya masu Mutum biyu da sharaɗin kowanne dole ne ya zamto yana da aiki tare kuma shaidar biyan haraji na shekaru biyu.

Kana kuma ta ɗaga shari'ar zuwa ranar 25 ga wata domin cigaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel