Kuda wajen kwadayi yakan mutu: An kama Trump da laifin bawa wata 'yar fim din batsa kudi don ta rufa masa asiri

Kuda wajen kwadayi yakan mutu: An kama Trump da laifin bawa wata 'yar fim din batsa kudi don ta rufa masa asiri

- Sabon Lauyan shugaban kasar Amurka Donald Trump, Rudy Giuliani ya tonawa maigidansa asiri, inda ya fallasa cewar ya baiwa wata jarumar fina-finan batsa ta kasar Amurka, Stormy Daniels, dalar Amurka dubu 130 do min ta rufa masa asiri

Kuda wajen kwadayi yakan mutu: An kama Trump da laifin bawa wata 'yar fim din batsa kudi don ta rufa masa asiri
Kuda wajen kwadayi yakan mutu: An kama Trump da laifin bawa wata 'yar fim din batsa kudi don ta rufa masa asiri

Sabon Lauyan shugaban kasar Amurka Donald Trump, Rudy Giuliani ya tonawa maigidansa asiri, inda ya fallasa cewar ya baiwa wata jarumar fina-finan batsa ta kasar Amurka, Stormy Daniels, dalar Amurka dubu 130 do min ta rufa masa asiri.

DUBA WANNAN: 'Yar shekara 19 ta lashe zaben kujerar Kansila

Wannan shine karo na farko da shugaban na kasar Amurka ya amsa laifin sa inda ya bayyana cewa yayi kokarin rufe bakin Stormy ne don kar ta fadawa duniya irin badakalar da suke aikatawa tare.

A watannin baya shugaba Trump ya karyata cewar babu wata alaka dake tsakanin sa da jarumar, sannan kuma bashi da wata masaniya game da dala dubu 130 da lauyan nasa Cohen yace ya bata a matsayin cin hanci. Amma kuma a yanzu sabon lauyan na Trump, Rudy Giuliani yayi magana a gidan talabijin na Fox, inda yace Trump ne ya baiwa Stormy wadannan kudaden.

A ranar Litinin dinnan data gabata, Stormy Daniels ta kai karar shugaba Trump kotu, inda take cewa ya Zage ta, sannan kuma yana kokarin shafa mata kashin kaji, alhalin ada can tare suke sheke ayar su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel